• English
  • Business News
Thursday, May 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Ni Da Burin Da Wuce Ziyarar Kabarin Manzon Allah – Fauziyya Sani

by Bushira Nakura
9 months ago
in Adon Gari
0
Ba Ni Da Burin Da Wuce Ziyarar Kabarin Manzon Allah – Fauziyya Sani
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

FAUZIYYA SANI JIBRIL, Marubuciya ce da ta samu nasarori da dama a harkar rubutu, a tattaunawarta da BUSHIRA A. NAKURA, ta bayyana dalilanta na shiga duniyar marubuta da kuma irin alheran da ta samu, kana ta bayyana babban burinta a rayuwa, inda ta ce babu abin da ta fi so a rayuwarta yanzu da ya wuce ta ziyarci kabarin shugaban halitta, kamar yadda za ku karanta.

A sha karatu lafiya

Assalamu alaikum, masu karatu za su ji cikakken sunanki da sunan da aka fi sanin ki da shi

Amin waalaikumussalam Warahamatullah wabarakatuhu. Sunana Fauziyya Sani Jibril, amma an fi sani na da Aunty Baby.

Za mu so jin Tarihin ki a takaice

Labarai Masu Nasaba

Ko Kin San… Yadda Ake Nagartaccen Tsumi?

Mata Mu Tsaya Da Kafafunmu Kar Mu Tsaya Sai An Bamu – Khadeejah Abdullahi

An haife ni a ranar 23 ga watan Nuwamba a shekarar 1989 a Unguwar Sudawa da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano. Na yi saukar Alkur’ani mai girma a makarantar Gwadabe Maitasa Islamiyya, na yi karatuna na Firamare a Makarantar Dandago Special Frimary School, na yi sakandiren ‘yan’mata ta Sanimainagge, karatuna na N.C.E kuma na yi shi ne a Aminu Kano College Of Education (AKCOE) inda na karanci Hausa Islamic

Kina da Aure in kina da shi ya’yan ki nawa?

Eh, ina da aure Allah ya albarkace ni da ‘ya’ya shida maza biyu mata hudu.

Zuwa yanzu kin ci gaba da karatu ne ko a’a?

Eh to yanzu dai ban ci gaba da karatu ba, amma ina da burin ci gaba in sha Allahu.

Kina sana’a ne ko aikin Gwamnati?

Ina sana’ar sayar da kayayyaki iri-iri wato ‘Collections’.

Wace irin Gwagwarmaya kika sha a rayuwarki?

Rayuwa ita kadai gwagwarmaya ce kuma kowa da irin tasa ko ga zaman gida aiki da rainon yara, kula da su da basu tarbiyya, wannan ma babbar gwagwarmaya ce, sai kuma wacce zan ce ba za ta wuce bangaren karatu da kuma wasu al’amuran na rayuwa ba kadan ba masu yawa.

Ya a kai kika fara rubutu kuma wadanne hanyoyi kika bi don ganin kin zama marubuciya?

Yadda aka yi na zama Marubuciya da kuma hanyoyin da na bi kafin na fara rubutu. To da farko dai rubutu burin mahaifiyata ne, Allah Ya cika mata wannan buri nata a kaina, ma’abociyar karatun littattafai ce don haka ta so zama Marubuciya, kuma tun muna kanana ta kan karanta mana littattafan da suka yi daidai da shekarunmu, ni ma na kan je na ba wa kawayena labarin da ta karanta mana, sai yadda suke jin dadin labarin ya dinga burge ni, da haka son yin rubutu ta darsu a zuciyata, burin yin rubutun ya karu ne dalilin karantar Hausa da na yi. Bayan na kammala karatuna na N.C.E sai na nemi yardar mijina da ta iyayena a kan ina son fara rubutu, bayan sun amince tare da saka min albarka, sai na nemi shawarar kawata abokiyar karatuna, shahararriyar Marubuciya wato Hassana Labaran Danlarabawa, ta nuna min jin dadinta tare da ba ni shawarwari. Daga nan sai ta saka ni a kungiyar Lafazi Writers Association, inda Malam Abubakar Sadik ya ci gaba da gwagwarmayar koyar da mu ka’idojin rubutu tare da dabarun rubuta labari. Ina fatan Allah Ya saka musu da mafificin alkairi.

Me ya baki sha’awa da har kika soma Rubutu?

Abin da ya ba ni sha’awa na fara rubutu, shi ne yadda marubuta suke samun damar isar da sako ga al’umma cikin sauki ta rubutunsu, kuma sakon ya yi tasiri fiye da yadda yake yi idan an bi ta wata hanyar wadda ba ta rubutun ba.

Kin taba fitar da littafi ne idan kin taba ki fada mana adadin littattafan da kika fitar da sunayensu?

A’a ban taba fitar da littafi nawa na kaina ba, sai na hadakar labaran da suka yi nasara a gasa, amma ina da niyyar fitar da nawan a nan kusa in sha Allahu.

To kenan ta ina sakon rubutunki ke isa ga al’umma?

Ina isar da sakon ne ta hanyar online wato ni online Writer ce.

Wadanne irin nasarori kika taba samu ta hanyar rubutun online?

Na samu nasarori da dama ta dalilin rubutu, na san manyan mutane, manyan Marubuta wadanda ba don ta dalilin rubutu ba zan san su ba, kuma na sha samun kyaututtuka daga masu karanta labaraina, da manazarta, sannan kuma na sha samun kyaututtukan kudi, katin waya, Data, da lambobin yabo daga bangarori da dama, haka kuma an sha gayyata ta a yi hira da ni a matsayina na marubuciya, an yi hira da ni a kungiyarmu ta Lafazi Writers Association, a shirin da ake gabatarwa na Mu San Juna, wanda Malam Abubakar da Asiya Muhammad suke gabatarwa. An yi hira da ni a gidan rediyon Dala FM cikin shirin Duniyar Marubuta wanda Malam Jibrin Adamu Rano yake gabatarwa a duk ranar Talata, bugu da kari ga shi a yanzu ana yin hira da ni, a wannan shahararriyar jaridar ta lEADERSHIP, cikin filin ADON GARI tare da ke Aunty Bushira Nakura, wanda hakan ba karamar nasara ce a gare ni ba.

Na san kin yi karance-karancen littattafan Hausa ko za ki iya fada mana littattafan su wa kika karanta?

Na karanta littattafan Marubuta da dama gaskiya, amma wadanda na fi karanta nasu, su ne: Baba Ado Ahmad Gidan Dabino, da kuma Aunty Fauziyya D. Sulaiman, Aunty Halima K/Mashi, Aunty Billy, Hassana Danlarabawa, Malam Jibrin Adamu Rano, Malam Abubakar Sadik, da kuma Malam Muttaka A. Hassan, da dai sauran su.

Cikin marubuta littafin wa ke birgeki wanda har yanzu in kika samu za ki so ki sake karantawa?

Akwai wasu daga cikin littattafai na Baba Ado Gidan Dabino da na Malam Jibrin Rano, da na Hassana Danlarabawa, har yanzu idan na same su zan kuma karanta su, saboda salon labarinsu yana da jan hankali kwarai.

Meye Burinki nan gaba wanda kike fatan ki cika shi?

Burina na gaba shi ne, in kawo sababbin abubuwa na cigaba a duniyar marubuta.

Ina da manyan burika a rayuwata, na farko ina da burin kara samun kusanci ga masoyina Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, sannan ina da burin samun damar da zan hidimta wa iyayena, iyalaina, ‘yan’uwana, da Musulmi baki daya, musamman mabukata da kuma marayu.

Akwai gasa da marubuta suke shiga ko kin taba shiga, in kin taba wace irin nasara kika samu?

Na taba shiga gasa daban-daban, Alhamdu lillah na samu nasarori masu yawa, daga ciki akwai ita kanta samun damar shiga gasar, sannan kuma na samu nasara a gasar wata-wata ta group din marubuta, inda na zama gwarzuwar wata da labarina mai suna MAULA. Haka kuma na samu nasara a gasar Marubuta Group, mai taken bincike, wadda aka gabatar da ita yayin cikar Group din shekara bakwai, inda na samu nasarar zuwa ta uku da labarina mai suna TUWON TULU, an buga labaran a littafi kuma an yi mini kyautar kudi da satifiket, bugu da kari na samu nasara a gasar wata-wata wadda kungiyarmu ta LAFAZI WRITERS ASSOCIATION take gabatarwa, inda na zama gwarzuwa da labarina mai suna KWANGE. Haka kuma na taba cin gasar musabakar Alkar’ani Mai Girma, wadda Zauren Marubuta ta shirya, na samu nasarar zuwa ta biyu. A duk gasar na samu kyaututtuka da shaidar karramawa, a yanzu haka akwai manyan gasa da na shiga kuma Alhamdulillah labaraina sun fito a zangon farko na gasar, ina fatan samun nasara a zangon karshe da yardar Allah.

Wane irin kalubalen Rayuwa kika taba fuskanta?

Na sha fuskantar kalubale iri-iri, domin ita rayuwa ba a raba ta da kalubale, amma alhamdulillah duk kalubalen da ya zo mini a rayuwa na kan bi shi da addu’a, don haka cikin sauki nake samun mafita.

Wane irin kalubale kika taba fuskanta a duniya rubutu ?

Gaskiya ban fuskanci wani kalubale a duniyar rubutu ba, illa bacewar rubutu dalilin lalacewar abin yin rubutun, kafin na samu wayewar taskance shi a ma’adana.

Me za ki iya fada game da rubutu?

Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah ala kulli halin. Hakika babu abin da zan ce wa rubutu domin ta dalilin rubutu nasan mutane da dama, nima kuma wasu sun sanni

Ta dalilin rubutu na samu nasarori masu tarin yawa don haka ni na ce rubutu alkairi ne ga mai yin sa, idan ya tsaftace alkalaminsa.

Wane irin albishir za ki yi wa makarantanki?

Ina yi wa masoya littattafaina albishir cewar nan ba da dadewa ba zan gabatar da wani littafi, wanda zai kawo sauyi da abubuwan ci gaba a rayuwa.

Su waye gwanayen ki cikin marubuta maza da mata?

Gwanayena cikin marubuta su ne: Baba Ado Ahmad Gidan Dabino, Malam Abubakar Sadik, Malam Jibrin Adamu Rano, Malam AbdulRahman Aliyu, Malam Muttaka A. Hassan, Malam Nura Isma’il Abu Othaymeen, Bamai Dabuwa, Muktar Musa Karami Abu Hisham, da sauran su.

Gwanayena a cikin Marubuta mata su ne: Aunty Halima K/mashi, Aunty Fauziyya D. Sulaiman, Aunty Billy Galadanci, Aunty Hassana Danlarabawa, Amira Souley, Maryam M. Sani, Nana Aisha Hamisu, Hadiza D. Auta, Surayya Dee. Hauwa Shehu, Fatima Alaramma, Fiddausi Sodangi, da sauran su

Nasiharki ga marubuta.

Nasiha ta ga Marubuta ita ce. Su ji tsoron Allah, su rubuta abin da zai zama mai amfani da kawo gyara a cikin al’umma, hakan zai amfane su har bayan rayuwarsu, domin a duk lokacin da aka yi amfani da abin da ka rubuta na taimakon al’umma za ka samu kamasho na lada, kamar yadda idan ka rubuta abin da bai dace ba na gurbacewar al’umma shi ma kana da kamasho na zunubi.

Wane abu ne wanda aka taba yi miki ko ya same ki na farin ciki wanda ba za ki taba mantawaba da shi ba?

Abin farin cikin da ba zan taba mantawa da shi ba shi ne. Yadda iyayena suka ba ni kulawa, Ilimi da tarbiyya wadda ni ma nake ba wa nawa ‘ya’yan, domin abin da kake da shi, shi kake bayarwa. Hakan yana faranta min rai kwarai, kuma ina addu’ar Allah Ya saka musu da gidan Aljanna, Ya ba ni ikon kyautata musu yadda ya kamata.

Wane abu ne na bakin ciki wanda shima ba za ki taba mantawa da shi ba?

Abin bakin cikin da ba zan mantawa ba shi ne. Yadda tsaro ya tabarbare a kasar nan, abin yana kona min zuciya, domin duk wani cigaban rayuwa yana damfare ne da zaman lafiya.

Me kikafi so ayi Miki kyauta da shi?

A yi mini kyautar kujerar Makka, in ziyarci dakin Allah da kabarin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam

Abin da nake son fada wanda ba a tambaye ni ba shi ne, yadda nake gudanar da rubutuna duk da hidimir maigida da ta iyali. Ina gudanar da rubutuna cikin dare ko bayan Sallar Asubah idan na gama addu’o’i da karatun Alkur’ani, a takaice dai ina ware wa komai lokacinsa, ibada, hidimar gida, da rubutu komai ina ware masa lokacinsa.

Fatan ki ga jaridar LEADERSHIP Hausa

A karshe fatana ga jaridar LEADERSHIP Hausa shi ne, ina yi musu fatan su ci gaba da samun daukaka, nasarori da alkairai masu tarin yawa.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Adon GariFauziyyaZiyara
ShareTweetSendShare
Previous Post

Tinubu Shugaba Ne Mai Son Ci Gaba Da Kuma Kishin Talakawa – Minista

Next Post

Matasa Sun Yi Warwason Motar Taki A Adamawa

Related

Ko Kin San… Yadda Ake Nagartaccen Tsumi?
Adon Gari

Ko Kin San… Yadda Ake Nagartaccen Tsumi?

2 weeks ago
Mata Mu Tsaya Da Kafafunmu Kar Mu Tsaya Sai An Bamu – Khadeejah Abdullahi
Adon Gari

Mata Mu Tsaya Da Kafafunmu Kar Mu Tsaya Sai An Bamu – Khadeejah Abdullahi

3 months ago
Mata Mu Dage Da Neman Ilimi Da Neman Na Kanmu -Hassana Umar
Adon Gari

Mata Mu Dage Da Neman Ilimi Da Neman Na Kanmu -Hassana Umar

4 months ago
Mata Ku Dage Da Karatu Domin Tallafa Wa Rayuwarku Da Ta ‘Ya’yanku – Zahra’u Adam
Adon Gari

Mata Ku Dage Da Karatu Domin Tallafa Wa Rayuwarku Da Ta ‘Ya’yanku – Zahra’u Adam

5 months ago
Nijeriya Da Brazil Sun Cimma Yarjejeniyar Bunkasa Noman Zamani A Kasar Nan
Adon Gari

Halima Aliko Dangote Ta Nemi A Ba Mata Damar Shiga Harkokin Kasuwanci Yadda Ya Kamata

5 months ago
Mata A Dage Da Karatu Yin Haka Taimakon Kanku Ne Da ‘Ya’yanku – Zainab Ahmad
Adon Gari

Mata A Dage Da Karatu Yin Haka Taimakon Kanku Ne Da ‘Ya’yanku – Zainab Ahmad

6 months ago
Next Post
Matasa Sun Yi Warwason Motar Taki A Adamawa

Matasa Sun Yi Warwason Motar Taki A Adamawa

LABARAI MASU NASABA

Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara

’Yan Bindiga Sun Sace Mutane 200 A Mazaɓa Ta A Zamfara – Ɗan Majalisar Tarayya

May 15, 2025
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba

’Yansanda Sun Cafke Mutane 9 Kan Kisan Jigon Jam’iyyar PDP A Adamawa

May 15, 2025
UTME

ASUU Ta Yi Barazanar Maka JAMB A Kotu Biyo Bayan Samun Mummunan Sakamako A UTME

May 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

May 14, 2025
Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

May 14, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

May 14, 2025
gaza

Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 1.78 Na Abuja Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa

May 14, 2025
Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

May 14, 2025
Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

May 14, 2025
Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

May 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.