Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake yi na cewa zai jagoranci gwamnoni biyar zuwa jam’iyyar adawa ADC.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Dauda Iliya ya fitar, ya bayyana labarin a matsayin jita-jita wadda ba ta da tushe ballantana makama kuma ya tabbatar da goyon bayansu ga jam’iyyar APC.
- Gwamna Zulum Ya Bayar Da Tallafin Miliyan 300 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Mokwa
- Zulum Ya Yaba Wa Sojoji Kan Kashe Babban Kwamandan ISWAP Abu Fatima
“Muna sane da jita-jitar da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta cewa ina shirin barin jam’iyyar APC domin komawa jam’iyyar ADC, tare da gwamnoni guda biyar”. In ji Gwamna Zulum
Ya ci gaba da cewa “Wannan labarin ƙanzon kurege ne da wasu suka tsara. Mutanen da suke yaɗa wannan labarin ba masu kishin jihar Borno bane, suna yaɗa labaran ne kawai domin kawar da hankalimu wajen aikin da muke yi wa al’umma”.
Ya ƙara da cewa “Goyon baya na ga jam’iyyar APC yana nan daram kuma na sadaukar da kaina wajen hidimtawa al’ummar jihar Borno. Ina roƙon al’umma da su yi watsi da wannan labarin. Bamu da lokacin yin irin wannan siyasar, mun mayar da hankali kacokan domin sauke nauyin da yake kanmu “.
Zalum ya kuma shawarci gidajen jaridu da su dinga tantance labarai kafin su yaɗa shi domin kaucewa labaran ƙanzon kuregen da wasu suke yaɗawa.
A ƙarshe gwamnan ya ce ya duƙufa wajen hidimtawa al’ummar jihar Borno a ƙarƙashin jam’iyar mai albarka ta APC .
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp