Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa burinsa shi ne zama gwamnan Kano, ba sake shugabantar jam’iyyar APC a jihar ba.
Abbas ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da BBC, inda yake mayar da martani kan kalaman Ministan Gidaje na Nijeriya, Yusuf Abdullahi Ata, wanda ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar APC idan Abbas ya sake zama shugaban jam’iyyar a karo na huɗu.
- Zan Fice Daga APC Matuƙar Abdullahi Abbas Ya Ci Gaba Da Zama Shugaba A Kano – Ministan Tinubu
- Matakin Amurka Na Takaita Zuba Jari Zai Cutar Da Wasu Da Ita Karan Kanta
A wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, Ata ya bayyana cewa zai fice daga jam’iyyar tare da magoya bayansa idan ba a sauya shugabancin APC a Kano ba, yana zargin Abbas da haddasa faɗuwar jam’iyyar a zaben 2023.
Sai dai Abbas ya ce Ata ba ɗan APC ba ne tun asali, kuma sun yi mamakin yadda aka naɗa shi minista. “A zaɓen da ya gabata a ƙaramar hukumarsa ma, mun zo na uku. Kuma ba mu sani ba aka ba shi muƙamin minista, har ma muka shaidawa shugaban ƙasa cewa ba ɗan jam’iyyarmu bane.”
Ya ƙara da cewa, “Muna mamakin yadda aka naɗa shi minista, domin ɗan siyasa ne na ƙaramar hukuma kawai.”
Barazanar Ata Kan Ficewa Daga APC
A cikin bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, Minista Yusuf Ata ya yi magana da magoya bayansa, yana mai cewa idan ba a sauya shugabancin APC a Kano ba, to zai fice daga jam’iyyar.
“Muna faɗa wa kowa, idan aka mayar da irinsu, duk irinmu fita za mu yi,” in ji Ata.
Ya ƙara da cewa, “Idan suka dawo da shi, za mu fice, kuma na rantse da Allah jam’iyyar za ta sake faɗuwa a zabe.”
Wannan rikici na ƙara nuna rabuwar kai a cikin APC a Kano, wanda ka iya shafar ƙarfi da tasirin jam’iyyar a jihar nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp