• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Sai Mace Ta Tallata Jikinta Za Ta Samu Kudi Ba – Amina Ishak

by Sulaiman
2 years ago
Mace

Amina Ishak Bako, matashiya ce kuma ‘yar kasuwa mai neman abin da za ta rufa wa kanta da iyaye ‘yan uwa da abokan arziki asiri, a cikin hirarsu da wakiliyar LEADERSHIP Hausa Maryam Aliyu Dankyalta bayan yadda ta tsunduma harkar kasuwanci da nasarorin da samu har ma da kalubalen da ke fuskanta, inda cikin kalamanta na jan hankali ta ce ba sai mace ta tallata jikinta za ta samu kudi ba. ga dai yadda hirar ta kasance:

Da fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki?

Suna na Amina Ishak Bako ni cikakakkiyar ‘yar Filato ce daga daga Karamar Hukumar Mangu, kuma ina zaune a cikin Garin Jos.

LABARAI MASU NASABA

Ko Kin San… Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al’adarsu?

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

Shin Amina matar aure ce?

A’a ni ba matar aure ba ce

To ‘yar kasuwa ce ko kuma ma’aikaciya ce?

Ni ‘yar kasuwa ce

Wanne irin kasuwanci kike yi? 

Gaskia Ina kasuwanci da dama amma abin da na fi ba da karfi shi ne saida dankalin turawa, kayan lambu, Kamfala da takalman maza da hulunan maza.

Me yaja hankalinki har kika shiga wannan kasuwancin?

Zaman banza ne ba na so, kuma saboda ina ganin idan ina sana’a zan fi karfin kudi sabulu da turare da sauran hidindimu ga kuma uwa uba zan iya taimaka wa mahaifiyana da hidimomin gida.

Nenene matakin karatunki?

Matakin karatu na Digiri.

Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a cikin sana’arki? 

Mutane da dama musaman wadanda suka sanni sai zu karbi kayana bashi ba za su biya ba har ya kai ga na samu karayar jari

Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika cimma?

Eh to yanzu gaskiya zan ce na yi nasara wajen taimaka wa mahaifiyata da wasu abubuwan.

Wanne abu ne yafi faranta miki rai game da sana’arki?

Gaskiya Alhamdullilah tun da a yanzu bani tambaya ko rokon wani taimako gun kowa kama daga kan ‘yan uwa zuwa ga saurayi saboda abin da ke kawo kaskanci kenan.

Ta wacce hanya kike bi wajen tallata sana’arki?

Ta intanet da dama kuma ‘yan uwa na taya ni tallata kayana zuwa ga abokan aikinsu da abokansu kuma suma masu sayen kayana Alhamdullilah suna gaya wa wasu akaina.

Dame kike so mutane su rika tunawa dake?

Ina so a tuna da ni ta fuskar abubuwa da dama, amma mafi muhimmanci shi ne mace ba lalle sai ta tallata jikinta kafin ta sami abin da take so ba, tare da aiki tukuru da juriya babu abin da ya gagara

Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?

Gaskia Alhamdullilah saboda ina samu goyon baya yadda ya kamata saboda suna nufina da abubuwa da dama

Kawaye fa?

Ina da kawaye amma yawanci wadanda muka hadu a makaranta ne muka zama abokai

Me kike fiso cikin kayan sawa da kayan kwalliya?

Ni ba ma’abociyar kwalliya bace amma ina son Abaya sosai da turare

A karshe wace irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?

Mata mu tashi mu kama sana’a tana hana sa ido

Na gode

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

tusar gaba
Adon Gari

Ko Kin San… Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al’adarsu?

August 31, 2025
Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa
Ado Da Kwalliya

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

August 3, 2025
Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa
Adon Gari

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

July 27, 2025
Next Post
Xi Jinping Ya Taya Shehbaz Sharif Murnar Zama Firaministan Pakistan

Xi Jinping Ya Taya Shehbaz Sharif Murnar Zama Firaministan Pakistan

LABARAI MASU NASABA

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.