Yau na karanta wata makalar da farfesa Bedassa Tadesse na jami’ar Minnesota ta kasar Amurka ya rubuta, wadda aka wallafa a shafin yanar gizo na “Conversation” na kasar Australiya. Cikin makalar ya ambaci wani abu mai ban sha’awa: Ko da yake masu nazarin ilimin tattalin arziki sun ce bambancin al’adu ya kan haifar da babban shinge ga cinikin kasa da kasa, amma bayan da aka yi nazari kan huldar ciniki tsakanin kasar Sin da sauran kasashe kusan 90, cikin shekaru 16 da suka gabata, an gano cewa, bambancin al’adu kusan bai yi tasiri kan cinikayyar kasar Sin tare da sauran kasashe ba.
To sai dai ko mene ne dalilin haka? A ganin farfesa Tadesse, dalili shi ne yadda kasar Sin ta iya daidaita burinta da na abokan hulda, musamman ma a fannin raya tattalin arziki. Ya ba da misalin nahiyar Afirka, inda ya ce ko da yake kasashe 54 dake nahiyar dukkansu na da mabambantan al’adu, da harsuna, amma bambancin bai taba hana kasar Sin yin ciniki da kasashen ba. Sa’an nan dalilin da ya sa hakan, shi ne kasar Sin ta samar wa kasashen Afirka da jarin da ake bukata wajen raya kayayyakin more rayuwa, da fasahohin zamani marasa tsada, da sharadi mai sauki na samun rance. Yayin da take hadin gwiwa da sauran kasashe, kasar Sin ta yi kokarin tabbatar da moriyar juna, da damar samun ci gaba tare, maimakon dabarar da kasashen yamma ke runguma ta barin kamfanoni su yi takara don neman riba.
- Xi Jinping Ya Gana Da Firaministan Hungary
- Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Nanata Bukatar Karfafa Jingar Kare Ambaliya Yayin Da Ake Kokarin Takaita Aukuwar Ambaliya A Kasar
A gani na, ra’ayin farfase Tadesse daidai ne, amma bai kai wani matsayi mai zurfi ba tukuna. Idan ya samu damar hira da dimbin ‘yan Afirka, zai fahimci cewa dalilin da ya sa kasar Sin ta samu karbuwa tsakanin kasashe masu tasowa, bai tsaya kan damar samun ci gaba da moriya a fannin tattalin arziki ba.
Alal misali, wajen taron tunawa da kaddamar da ka’idoji 5 na tabbatar da zama tare cikin lumana a duniya, wanda ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin a kwanan baya, Chales Onunaiju, darektan cibiyar nazari kan kasar Sin ta Najeriya, ya ba da jawabin cewa, babu ainihin adalci a duniyarmu, inda ya tsamo maganar sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken, wato “Idan ba ka zauna a gaban teburin cin abinci ba, to, za ka zama cikin jadawalin oda.” Sai dai ta yin la’akari da yanayin da ake ciki, mene ne abun da ya kamata su kasashe masu tasowa su yi? A cewar mista Onunaiju, kamata ya yi “a yi abun da kasar Sin ta yi, wato raya kai don neman samun karuwar karfin kasa.” Ya ce, “ idan an zaci za a samu adalci ta hanyar yin kira, to, abun da ke faruwa a yankin Gaza zai nuna maka cewa ba haka ba ne. A wannan zamanin da muke ciki, duk wata kasa, mai kaunar kasar Sin, ko akasin haka, ba za ta iya kyamarta ba. ” Ya ce, “Dole ne mu zama masu karfi, ta yadda ba za mu nemi a tausaya mana ba, maimakon haka za mu iya dogaro da kai.” Ta wadannan kalmomin Mista Onunaiju, za mu gane cewa, wani babban dalilin da ya sa kasar Sin samun karbuwa tsakanin kasashe masu tasowa, shi ne yadda ta zama abin koyi ga sauran kasashe, a fannin kokarin raya kai, ta yadda ta zama wata kasa mai karfin tattalin arziki cikin nasara.
A dai taron na tunawa da kaddamar da ka’idoji 5 na zama tare cikin lumana, tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Kgalema Motlanthe ya zanta da manema labaru, inda ya ambaci yadda kasashen yamma suke raba kafa dangane da manufofinsu. A cewarsa, “Manyan kasashe masu karfi su kan saka wa sauran kasashe takunkumi, da haraji na hukunci. A sa’i daya kuma, suna bukatar kasashe marasa karfi da su bude kofar kasuwanninsu, wai bisa ‘ka’idojin kungiyar ciniki ta duniya WTO’. Ya ce ya kamata ka’idojin su zama bisa adalci, amma su kasashe masu karfi ba su taba bude kofa kamar yadda suke bukatar sauran kasashe su yi ba.” Sai dai a halin yanzu, a ganin mista Motlanthe, kasar Sin ta samar da sauye-sauyen yanayi. Ya ce, “Kasar Sin ta nuna dabara mai dacewa ta raya al’umma. Bisa matsayinta na babbar kasa mai karfin tattalin arziki, wadda ke kokarin zamanantar da kai, kasar Sin ba ta neman yin babakere a duniya. Maimakon haka, tana kokarin kulla huldar hadin kai tare da kananan kasashe cikin daidaito, da fatan ganin ci gaban al’ummar dan Adam ta bai daya, ba tare da barin wasu gungun mutane a baya ba. A gani na, dabarar kasar Sin tana da matukar muhimmanci ga daukacin dan Adam.” Ga shi dai mista Motlanthe ya bayyana daya daga cikin manyan dalilan da suka sanya kasar Sin samun karbuwa: Wato kasar Sin ta yi watsi da tsohon tsarin kasa da kasa na kashin dankai, inda take wakiltar sabon tsari na daukaka adalci da daidaito.
Masana na kasashen yamma irin su Bedassa Tadesse, suna ganin yadda kasar Sin da sauran kasashe masu tasowa suke cude-ni-in-cude-ka, amma sun kasa fahimtar buri, da bukatu na bai daya na wadannan kasashe. Sai dai batun nan na biyu, shi ne dalili mafi muhimmanci da ya sanya kasar Sin samun karbuwa sosai tsakanin kasashe masu tasowa. (Bello Wang)