ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, November 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba ‘Yan Nijeriya Ne Ke Kai Mana Hare-hare A Benuwai Ba – Gwamna Alia

by Sadiq
7 months ago
Benuwai

Gwamnan Jihar Benuwai, Reverend Father Hyacinth Alia, ya bayyana cewa wasu maharan da suka kai hari a jihar ba ‘yan Nijeriya ba ne.

Yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Gwamna Alia ya ce irin harshen da maharan ke amfani da shi – Hausa da Fulatanci – ba irin wanda ake amfani da shi a Nijeriya ba ne.

  • Rashin Jituwa Tsakanin Amurka Da China Na Iya Jefa Tattalin Arziƙin Duniya Cikin Hatsari – IMF
  • Sabuwar Ƙungiyar ‘Yan Bindiga Ta Addabi Jihohin Kwara Da Neja

Ya ce: “Sun zo ne ɗauke da makamai irin su AK-47 da AK-49, kuma ba sa magana kamar yadda mu ‘yan Nijeriya muke yi. Harshensu daban ne.”

ADVERTISEMENT

Gwamnan ya ƙara da cewa bayanan da suka fito daga mutanen yankunan da aka kai wa hare-haren sun tabbatar da cewa maharan ba ‘yan Nijeriya ba ne.

Wannan jawabi ya fito ne bayan ziyarar da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Nuhu Ribadu, ya kai jihar domin nuna alhini da kuma tabbatar wa da al’umma cewa gwamnati na ɗaukar matakai don shawo kan matsalar tsaro.

LABARAI MASU NASABA

PDP Ba Ta Mutu Ba Duk Da Rikicin Da Ta Ke Fama Da Shi – Anyanwu

Ana Zargin ’Yan Ta’adda Sun Kashe Janar Ɗin Soji A Harin Kwanton-Ɓauna A Borno

Ba wannan ne karon farko da ake zargin wasu ‘yan ƙasashen waje da kai hare-hare a Nijeriya ba.

A baya an yi zargin cewa ƙungiyoyi kamar Lakurawa da ke kai hare-hare a jihohin Sakkwato da Zamfara, sun samo asali ne daga ƙasashen waje.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

PDP Ba Ta Mutu Ba Duk Da Rikicin Da Ta Ke Fama Da Shi – Anyanwu
Manyan Labarai

PDP Ba Ta Mutu Ba Duk Da Rikicin Da Ta Ke Fama Da Shi – Anyanwu

November 18, 2025
Ana Zargin ’Yan Ta’adda Sun Kashe Janar Ɗin Soji A Harin Kwanton-Ɓauna A Borno
Manyan Labarai

Ana Zargin ’Yan Ta’adda Sun Kashe Janar Ɗin Soji A Harin Kwanton-Ɓauna A Borno

November 18, 2025
Bukatar Samar Da Cikkakken Tsaro Ga Hukumar Zabe
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi

November 18, 2025
Next Post
Rage Mace-Macen Mata Da Jarirai: Kasar Sin Ta Ba Da Kyakkyawan Misali Ga Kasashe Masu Tasowa

Rage Mace-Macen Mata Da Jarirai: Kasar Sin Ta Ba Da Kyakkyawan Misali Ga Kasashe Masu Tasowa

LABARAI MASU NASABA

PDP Ba Ta Mutu Ba Duk Da Rikicin Da Ta Ke Fama Da Shi – Anyanwu

PDP Ba Ta Mutu Ba Duk Da Rikicin Da Ta Ke Fama Da Shi – Anyanwu

November 18, 2025
Shugabar Tanzania Ta Bai Wa ’Yarta Da Sirikinta Muƙamin Minista

Shugabar Tanzania Ta Bai Wa ’Yarta Da Sirikinta Muƙamin Minista

November 18, 2025
Ana Zargin ’Yan Ta’adda Sun Kashe Janar Ɗin Soji A Harin Kwanton-Ɓauna A Borno

Ana Zargin ’Yan Ta’adda Sun Kashe Janar Ɗin Soji A Harin Kwanton-Ɓauna A Borno

November 18, 2025
Bukatar Samar Da Cikkakken Tsaro Ga Hukumar Zabe

’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi

November 18, 2025
Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 

Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 

November 17, 2025
Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

November 17, 2025
Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas

Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas

November 17, 2025
An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing

An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing

November 17, 2025
NBS

Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065%

November 17, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

November 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.