Yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum.
Da take magana dangane da karfin nuna babakere na Japan a kokarinta na tafka abin da ya saba da “Kundin tsarin mulkinta na zaman lafiya” da kuma ci gaba da bin hanyar fadada ayyukan soji, Mao Ning ta nuna cewa, shekaru 80 da suka gabata, ra’ayin nuna karfin soja na Japan ya haddasa yaki na zalunci, wanda ya haifar da babban bala’i ga yankin Asiya da ma duniya baki daya. A yau kuma, shekaru 80 bayan haka, ba za mu amince da farfado da ra’ayin nuna karfin soja na Japan ba.
- Wani Mai Taɓin Ƙwaƙwalwa Ya Kashe Soja A Legas
- Sin: Ya Zama Wajibi A Dakile Mummunan Yanayin Wanzuwar Tashe-tashen Hankula Da Yunwa
Game da matsalolin da aka samu a dangantakar Sin da Japan yanzu kuwa, Mao Ning ta ce, matsalolin sun samo azalai ne daga kalaman da firaministar Japan Takaichi Sanae ta yi game da Taiwan, wadanda ke zama babban tsoma baki a harkokin cikin gida na Sin. Kuma dole ne Japan ta janye kalamanta na kuskure nan take, ta canza matakin da ta dauka, kuma ta bai wa jama’ar Sin cikakkiyar amsa.
Mao Ning ta kuma bayyana cewa a yau, Liu Jinsong, shugaban hukumar kula da harkokin Asiya ta ma’aikatar harkokin wajen Sin, ya yi shawarwari da Masaaki Kanai, shugaban hukumar kula da harkokin yankin Asiya da Pasifik ta ma’aikatar harkokin wajen Japan a Beijing.
A yayin shawarwarin, Sin ta sake nuna matukar rashin amincewa da kalaman da firaministar Japan Takaichi Sanae ta yi game da Sin.
Bugu da kari, a game da amincewa da wani kuduri da kwamitin tsaron MDD ya yi kan zirin Gaza kuwa, Mao Ning ta bayyana cewa, daftarin kudurin da Amurka ta fitar bai yi cikakken bayani kan muhimman batutuwa game da shirye-shirye bayan yaki a zirin Gaza ba, kuma bai nuna cikakkun muhimman ka’idoji kamar “Falasdinawa ne ke mulkin Falasdinu” da shirin kafa “kasashe biyu” ba. (Safiyah Ma)














