Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bukaci kwamishinonin hukumar da ke kula da jihohi da su tabbatar an gudanar da zabe cikin inganci da nagarta.
Yakubu wanda ya shaida hakan a lokacin ganawa da kwamishinonin hukumar jiya a Abuja, ya ce, ba zai lamunci wani uzuri na kuskure ba, ya gargadesu da cewa duk wata gazawa da aka samu a kowace jiha, to kuwa kwamishina din da ke kula da wannan jihar shi zai dauki alhakin hakan, don haka kowa ya ke ya yi aiki tukuru domin tabbatar da ingancin zabe.
- Wike Bai Taimake Ni A Zaben Shugaban Kasa Ba -Peter Obi
- Kotu Ta Daure Babban Odita-Janar Na Jihar Yobe Kan Almundahanar Kudi
Babban Sakataren watsa labarai na shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi a hirarsa da LEADERSHIP a Abuja jiya, ya ce, an yi ganawa da kwamishinonin zaben ne domin tattaunawa da muhawara ta karshe kan shirye-shiryen zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi tare da zabukan cike gurbi da za a gudanar ranar 18 ga watan Maris.
Ya ce, kwamishinonin sun tabbatar da cewa za su zage damtse su yi aiki tukuru domin gudanar da sahihin zabe, ingataccen, mai cike da gaskiya da adalci kuma cikakken zabe.
LEADERSHIP ta gano cewa, an kira ganawar ne domin tattauna hanyoyin da za a bi domin kauce wa matsaloli wajen daura sakamakon zaben kamar yadda aka samu a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya zuwa shafin shigar da sakamakon zabe (IReV).