A safiyar yau Laraba ne kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC da daukacin kungiyoyin ta suka fara gudanar da gangamin neman kawo karshen zanga-zangar da ta shafe kwanaki biyu tana yi a fadin kasar.
Zanga-zangar dai na son gwamnatin tarayya ta warware duk wasu matsalolin yajin aikin ASUU.
- Hukumomi Sun Tsare Mahaifin Da Ya Sayar Da ‘Ya’Yansa Zabiya A Mozambique
- Babu Mafita Yanzu Game Da Karancin Man Jiragen Sama – Hadi Sirika
Da yake jawabi ga ma’aikata a Unity Fountain da ke Abuja a ranar Laraba, shugaban kungiyar NLC na kasa, Kwamared Ayuba Wabba, ya dage cewa majalisar ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta har sai gwamnatin tarayya ta warware duk wasu matsalolin da ke addabar jami’o’i.
Kwamared Wabba ya ce babu wani dalili da zai ’ya’yan talakawa su zauna a gida sama da watanni biyar yayin da yaran masu hannu da shuni ke karatu a kasashen waje.
Ya ce, “Babu hujja a kan wannan lamari, idan gwamnati ba ta shirya magance matsalolin ba, ba za mu gaji ba, dole ne mu fusata kan rashin nuna kulawar gwamnati.
“Wannan shi ne mafari, dole ne ku kasance a shirye don ceto fannin ilimi, mun gaji da cin kashin gwamnati kuma dole ne mu dauki makoma a hannunmu.
“Sun ce mu barazana ce ga tsaro amma matakin da suka dauka barazana ce ga dimokuradiyya, sai mun ja hankalinsu don ganin shugabanninmu sun yi abin da ya dace.
Ya kara da cewa, “Muna yabawa gwamnonin da suka fito don tattaunawa a jiya, muna son samun mafita kuma muna son a warware matsalar, ba za mu bari wasu tsiraru su ruguza makomar yaran Nijeriya ba.”
Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana cewa dole ne gwamnatin tarayya ta aiwatar da tsarin biyan albashin malaman jami’o’in na UTAS.