Shugaba Bola Tinubu ya ce babu wani daga cikin wadanda aka nada da za a bari ya bayar da uzuri ko hanzari na rashin gudanar da ayyukan da aka dora masa.
A jawabinsa na sabuwar shekara da ya yi wa ‘yan kasar a ranar Litinin a Legas, Tinubu ya ce ya yi alkawarin yi wa kasa hidima kuma zai bayar da duk abin da ya dace don amfanin al’ummar Nijeriya.
- Tinubu Ga Gwamnoni: Dole Ne Mu Tabbatar Da Zaman Lafiya A Nijeriya
- Tinubu Ya Yi Allah-Wadai Da Harin ‘Yan Ta’adda A Filato
“Dalilin da ya sa na samar da sashen auna nagartar aiki da sa ido shi ne, don shugaban kasa ya tabbatar da cewa ayyukan gudanar da mulki sun inganta rayuwar al’ummarmu.
“Mun saita tsari don tantance nagartar aiki a tsakanin rabin shekara da farkon wannan sabuwar shekara a ofishohin Ministoci da shugabannin hukumomin da ke karkashin wannan gwamnati da nake jagoranta don ganin sun ci gaba da nuna kwazon su.