Sabon ministan cikin gida da aka nada, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, zai dauki matakin kawar da duk wani jinkiri da ake samu wajen samar da fasfo da hukumar kula da shige da fice NIS ke yi, inda ya bayyana cewa, wadannan kwanakin sun shude ba za su sake dawo wa ba.
Minista Tunji-Ojo, ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar farko da ya kai hedikwatar NIS da ke Abuja a ranar Laraba 30 ga watan Agusta, 2023. Inda ya yi bayani da kakkausar murya da cewa ” ‘yan Nijeriya ba za su lamunci ci gbaa da samun jinkiri wajen samun fasfo ba. Samun fasfo wani hakki ne na ‘yan kasa, ba wata gata ba ce daban akan daidaiku,” in ji shi.
Ministan ya bayyana cewa, an kafa wani kwamiti da ya kunshi jami’an NIS da wakilan ma’aikatar harkokin cikin gida domin yin nazari mai zurfi don nemo mafita ga kalubalen da suke kawo tarnaki wajen samar da fasfon akan lokaci.
A jawabinta na maraba, mukaddashiyar Babbar kwanturola ta Hukumar NIS, Caroline Wura-Ola Adepoju, ta yiwa ministan karin haske kan ayyukan hukumar da kuma kalubalen da hukumar ke fuskanta.
Mukaddashiyar CGI, ta jadda goyon bayanta ga muradun Minista, inda ta ce, Hukumar NIS za ta baiwa Minista cikakken hadin kai domin tabbatar da samun nasara akan kudurinsa.