Kwanan baya, ma’aikatar cinikayya ta kasar Amurka ta fitar da wani bayani dake cewa za ta hana sauran kasashen duniya yin amfani da sashen harhada na’urorin laturoni na Chips kirar kasar Sin, ciki har da wanda kamfani Huawei na Sin ke kerawa wato “HUAWEI Ascend”.
Wannan yunkurin na Amurka da cin zali daga bangare guda, da baiwa kasuwa kariya, matakai ne wadanda tabbas za su illata matsaya daya da manyan jami’an Sin da Amurka suka cimma a kwanan baya, da moriyar kamfanonin kasar Sin, da kuma tsarin ayyukan masana’antun kira, da rarraba sassan semiconductor na duniya. Haka kuma, hakan zai hana sauran kasashen duniya zarafin raya fasahohin zamani, lamarin da ya sa gamayyar kasa da kasa zargin kasar Amurka kan batun.
- Masanan Najeriya Sun Bayyana Muhimmancin Hadin Gwiwar Afirka Da Sin A Fannin Tinkarar Kalubalen Harajin Kwastam Na Amurka
- Modric Zai Bar Real Madrid Bayan Kammala Gasar Cin Kofin Duniya Na Kungiyoyi
Matakin da kasar Amurka ta dauka, ya nuna cewa, tana son bunkasa ita kanta kawai, amma ba ta yarda sauran kasashen duniya su nemi nasu ci gaba ba, lamarin da ya saba da salon bunkasar kimiyya da fasaha na duniya. Ko shakka babu kuskuren da Amurka ta yi zai illata tsarin ayyukan masana’antun kira, da rarraba Chips na duniya, domin ba kawai zai kara farashin kayayyaki masu nasaba da hakan ba ne, da dakile ayyukan kirkire-kirkiren fasaha, har ma zai gurgunta moriyar kamfanoni da al’ummomin Amurka ita kan ta.
Kasar Amurka tana fatan ci gaba da kasance gaba a fannin yin kirkire-kirkire a fannin fasahar AI, amma, ba ta himmatuwa wajen daidaita kasuwanninta, da neman daukar karin masana, da kuma karfafa nazarinta, daidai kawai son bata yanayin da kasashen waje ke ciki.
Tabbas ba zai yiwu kasar Amurka ta samu ci gaba bisa wannan salo ba, maimakon haka matakan za su rage mata karfi, tare da haifarwa ita kanta illa. Abubuwan da suka faru sun nuna cewa, ba wanda zai iya hana ci gaban kasar Sin. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp