Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da duk wani nau’in cin hanci da rashawa ko rashin tausayi daga mambobin majalisarsa ba da ma’aikatan gwamnati a jihar ba.
A ranar Alhamis ne, gwamnan ya jagoranci zaman majalisar zartarwa na musamman a zauren majalisar da ke gidan gwamnatin jihar a Gusau.
- Minista Kyari, Gwamna Nasir Sun Kaddamar da Shirin Noma Na KADAGE A Kebbi
- Jimillar Kayayyakin Yau Da Kullum Da Aka Sayar A Sin A Shekarar 2023 Ta Zarce Yuan Triliyan 47
Babban mataimaki na musamman ga gwamna Dauda kan yada labarai, Sulaiman Bala Idris ne, ya bayyana haka a takardar da ya sanya ga manema labarai a Gusau.
A cewarsa Gwamna Dauda Lawal ya bukaci dukkan masu manyan mukamai da kwamishinoni da Shugabanin Kananan hukumomin da masu ba da shawara na musamman da ma’aikata su fahimci manufarsa tare da yin gyare-gyaren da suka dace.
“Dole ne mu kawo canjin da ake bukata domin ciyar da jihar gaba; dole ne mu yi abubuwa daban na kyawawan halaye.
“Ba al’ummar jihar ta zabe mu ba don kawai mu maye gurbin fuskoki da halayen wadanda suka gabace mu ba. An zabe mu ne don mu canza yadda ake gudanar da harkokin gwamnati, hanyar da za ta sa mu ci gaban al’umma.”
Gwamnan ya kara nanata wa majalisar zartarwar, cewa ba mun kawo kh ba ne cikin gwamnati don neman kudi.
“Game da haka, ina fada muku duk a yau, ba zan yarda da duk wani aiki na cin hanci da rashawa da rashin tausayi daga kowane mukami ko ma’aikacin gwamnati ba. Na sha cewa ban zo nan don neman kudi ba, kuma duk wanda ke da burin arzuta kan sa gara ya canza shawara ko kuma ya yi murabus daga gwamnati cikin mutunci.
“Kamar yadda na fada a baya, mun zabi kowannen ku ne bisa halayenku. Muna sa ran za ku yi sadaukarwa don canza jiharmu.
“Ba za mu iya cimma wani abu mai yawa ba idan ba mu sake duba ma’aikatan gwamnati da na ma’aikatanmu ba. Ina da niyyar gabatar da kuma sanya ma’aikatan gwamnati abin koyi da zai zama silar ci gaban jiharmu.
“Ina kira ga shugaban ma’aikatan gwamnatin jiha da su gaggauta samar da wata shawara mai amfani kan yadda za a sake fasalin ma’aikatan gwamnati tare da aiwatar da shi zuwa matakin inganci.
“Yayin da nake gyare-gyare a hidimar, ina da niyyar inganta ma’aikatanmu. na shirya horar da ma’aikatanmu na gida da waje.”