Kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola ya bayyana cewar, ba zai gaggauta sanya manyan ‘yan wasansa – Erling Haaland da Kevin De Bruyne a wasannin da kungiyar zata buga ba sakamakon raunin da suke fama dashi ba.
Guardiola ya bayyana hakan ne ga ‘yan jarida a ranar Juma’a yayin da yake jawabi gabanin wasan da City zata buga da kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace a ranar Asabar.
- Baya Ta Haihu: INEC Ta Rushe Babban Taron Jam’iyyar LP Na Kasa
- Kungiyar Hada-hadar Kasuwanci Da Ciniki Ta Sin Da Amurka Sun Gudanar Da Taron Mataimakan Ministoci Na Farko
Dukkan ‘yan wasan biyu, basu buga wasan da City ta lallasa Aston Villa da ci 4-1 a ranar Laraba ba, inda Guardiola yace, ya yi hakan ne sakamakon raunin da suke fama dashi kuma suke kan murmurewa.
City zata yi tattaki zuwa filin wasa na Santiago Bernabeu da ke birnin Madrid na kasar Sifaniya domin fuskantar Real Madrid a wasan farko na zagayen 16 na gasar zakarun Turai a mako mai zuwa.