Gwamnan Jihar Kogi mai barin gado, Yahaya Bello, ya yi alkawarin ba zai yi katsalandar a gwamnatin Usman Ododo ba.
“Babu wanda ya yi katsalandar a gwamnatina, domin haka b azan yi a na Ododo ba. Jama’a sun gamsu da ni. Ododo Ahmed Usman shi zai gudanar da gwamnati da kansa ko ta yi kyau ko mara kyau shi ne mai daukar alhakki,
- Muna Rokon Shugaba Tinubu Ya Hana Ministoci Tafiye-tafiye Zuwa Kasashen Waje – Akpabio
- An Haramta Shan Sigari A Wuraren Shakatawa Da Makarantu A Faransa
Bello ya shaida wa manema labarai na fadar gwamnati a lokacin da Ododo da gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, suka amshi takardar shaidar samun nasarar zabe da suka gabatar wa Shugaban kasa, Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja.
Sai dai ya yi kira ga al’ummar jihar da su bai wa sabon gwamnati mai zuwa hadin kai.
Ododo da Uzodimma sun gabatar da takardar shaidar lashe zabe ga Tinubu domin nuna godiya da irin shugabancin da yake gudanarwa tun bayan da ya zama shugaban kasa.
Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje, shi ne ya gabatar da takurdun shaidar ga Tinubu.
Da yake magana a kan nasarar da ya samu a wa’adi na biyu, gwamnan Jihar Imo, Mista Hope Uzodimma, ya ce nasarar da ya samu a zaben ranar 11 ga watan Nuwamba, ta kara tabbatar da nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a zaben shugaban kasar da kuma yadda jam’iyyar APC ke kara samun karbuwa a wajen ‘yan Nijeriya.
Ya kara da cewa cewa, “Kun tuna cewa a zaben ranar 11 ga watan Nuwamba babbar jam’iyyarmu ta APC ta samu tagomashi kuma ta samu nasara a Jihar Kogi da kuma Jihar Imo, sannan jagoran jam’iyyarmu shi ne shugaban kasa. A bisa al’adar a duk lokacin da muka karbi takardar shaidar cin zabe a matsayin gwamnonin jihohin Kogi da Imo, dole ne mu karrama shugaban kasa ta hanyar kawo masa takardar shaidar basai irin shugabancinsa da jagorancin da ya nuna tun bayan hawansa shugabancin kasar nan.