Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta taba yin sulhu ko sasanci da ‘yan bindiga ba.Â
Raddaa ya yi wannan ikirarin ne a lokacin taron addu’o’i na musamman da gwamnati jihar Katsina ta shirya domin samun saukin matsalar tsaro da ake fama da ita a jihar tuntuni.
- An Kammala Harhada Tushen Sashe Na SMR A Sin
- Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka Na Kara Haifar Da Da Mai Ido
Ya yi karin haske da cewa zai iya sauraren dan bindigar da ya ajiye makaminsa ya yadda ya rungumi zaman lafiya kuma ya zauna cikin al’umma to za a mayae da shi kuma za a saurare shi.
“Duk dan bindigar da bai yadda da zaman lafiya ba, zamu sa kafar wando daya da shi, kuma ba zamu saurara masa ba,” in ji shi.
Ya ce za su duk mai yiwuwa wajen ganin sun yi maganin ‘yan ta’adda da suka hana jama’a zaman lafiya ta hanyar karfafa jami’an tsaro da ba su kayan aiki da duk wani taimako da suke bukata.
Sannan ya yi kira ga jama’a da su je kai tsaye gidan gwamnatin jihar Katsina domin ba da bayanan sirri da za su taimaka wajen maganin duk wanda ke da hannu a wannan ta’adanci.
Gwamnan na Katsina ya shiga jerin ayarin jami’an tsaro da ke Katsina domin yin farautar kauraye a cikin garin Katsina da suke kwancen waya a hannun jama’a har kwana biyu a jere.
Haka kuma gwamnan ya yi kira ga daukacin al’umma da su ci gaba da yin addu’o’i da kaskantar da kai wajen Allah domin samun nasarar matsalar tsaro da ake fama da ita.
Kazalika, ya bai wa jama’a hakuri a kan halin kuncin da aka shiga na rayuwa, inda ya ce yanzu shirye-shirye sun yi nisa domin raba abinci kyauta ga ma bukata.
“Za mu raba wannan abinci a dukkanin runfunan zabe da muke da su a fadin jihar Katsina domin sauÆ™aÆ™awa jama’a halin kuncin da ake ciki na rayuwa,” in ji gwamnan.
Gwamnan ya yi karin haske dangane da matsalar da ke faruwa tsakanin gwamnatin Nijeriya da kuma kasar Nijar da ta fuskanci juyin mulki, inda ya ce nan gaba kadan za a samu maslaha in Allah ya yarda.