• English
  • Business News
Tuesday, July 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Taka-tsan-tsan A Kan Shirin Daukar Matakin Soja A Nijar

by Leadership Hausa
2 years ago
in Manyan Labarai
0
Gwamnatin Sojin Nijar Ta Yi Sabbin Nade-Nade
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

NiMet Ta Yi Hasashen Cikin Watan Yulin 2025 Za A Tabka Ambaliyar Ruwan Sama A Jihohin Nijeriya 19

Shafin Yanar Gizo Na ADC Ya Tsaya Cak Saboda Ɗumbin Magoya Baya Masu Son Yin Rijista

Guguwar juyin mulki da ta keta yankin Afirka ta Yamma tana bayar da mummunar alama watsi da tsarin dimokradiyya sannnu a hankali. A ra’ayinmu yadda ake neman a dawo da tsarin mulkin sojoji a tsakanin kasashe  yankin Afiika ta Yanma abu ne mai tayar da hankali kuma bai kamata a amince da shi ba.

Yankin da ke fuskantar ayyukan ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga yana kuma neman ya fuskanci juyin mulkin sojoji. Tuni aka hambarara da gwamnatin dimokradiyya ta kasashen Mali, Guinea da kuma Burkina Faso. Yanzu kuma sai ga shi a kasar Nijar.

  • An Kammala Harhada Tushen Sashe Na SMR A Sin
  • ECOWAS Ta Bada Umarnin Daukar Matakin Soji A Kan Gwamnatin Nijar

Wannan juyin mulkin da ya haska kasar Nijar a duniya ya faru ne a yayin da gungun sojoji a karkashin jagorancin dogarin shugaban kasa, Abdourahmane Tchiani, suka hambarar da zababben shugaban kasa Mohammed Basoum daga karagar mulki.

Nijar dai kasa ce mai fadin murabba’in kilomita 1,270,000 (Mil 490,000), wanda ya mayar da ita kasa mafi fadin kasa a yankin Afrika ta Yamma. Fiye da kashi 80 na kasar na mamaye ne da sararin sahara. Yawancin al’ummar kasar musulmai ne wadanda an kiyasta cewa sun kai mutum Miliyan 25. Kasar ta dade tana fama da kungiyoyin ‘yan gwagwarmayar addinin musulunci guda 2 da suka hada da wanda ta taso daga kasar Mali a shekarar 2015, da dayar da ta shigo daga Arewa maso gabashin in Nijeriya. Saboda haka ne a lokacin da labari ya iso na cewa, an sake samun juyin mulki a kasar Nijar, juyin mulki na uku kenan a yankin a cikin shekara 3 dole hankalin al’ummar duniya ya tashi.

A martaninsu, kungiyoyin ECOWAS, UN, EU, AU da saura kasashen duniya sun yi watsi da karbar mulki ta hanyar juyin mulki sun kuma garkama wa Nijar takunkumi daban-daban. Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, a martanisa ya yi tir da juyin mulkin ya kuma yi watsi da duk wani kokarin kwace mulki ta hanyar da ba ta dimokradiyya ba musamman hanyoyin da za su yi barazana ga zaman lafiya da tsarin mulkin dimokradiyya a Nijar. Ya kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su kai zuciya nesa su kuma tabbatar da sun kare tsarin mulki gaba daya.

A taronsu karo na 55 da suka yi a Abuja, shugabannin kungiyar ECOWAS sun garkama wa kasar Nijar takunkumin da suka hada da kulle dukkan iyakokin kasar ta kasa da ta sama a tsakaninta da dukkan mambobin kungiyar, a wannan taron ne kuma suka zartar da ba gwamnatin sojojin masu juyin mulki wa’adin kwanaki bakwai na su dawo da Shugaban Kasa Muhammed Bazoum karagar mulki.

Kungiyar ta ECOWAS ta kuma dora wa Nijar takunkumin kwace kaddarorinta a bankunan da ke kasashe mambobin ECOWAS tare da haramta wa kasar zirga-zirga a tsakanbin kasashen kungiyar ECOWAS ta jiragen sama da kuma ta kasa.

Amma kuma sojojin da suka yi juyin mulkin sun yi watsi da matsin lambar da ake yi musu, sun kuma ci gaba da garkuwa da Shugaba Basoum. Yayin da shugaban sojojin dan shekara 62, Tchiani, ya sanar da nada kansa a matsayin shugaban rikon kwarya na gwamnatin Nijar. Masu juyin mulkin sun ce sun yi hakan ne saboda yadda kasar ke neman tarwatsewa a sannu a hankali. Sun zargi shugaban kasar a kan rashin iya tafiyar da matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar da kuma yadda fatara da talauci suka addabi ‘yan kasa saboda tabarbarewa tattalin arzikin kasar.

A martaninsa game da juyin mulkin, Shugaba Bola Tinubu, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ECOWAS, ya ce, ba za a yarda da canjin gwamnati ta hanyar da bata dace ba, kuma ba za a yarda da hakan ba a dukkan kasashen Afrika, musamman ganin hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin ganin a daidaita al’amurra a yankin tare da dawo da tsarin dimokradiyya da mulki na gari.

Bayan karewar wa’adin da kungiyar ECOWAS ta ba jagororin juyin mulkin, sun yi gargadin cewa, duk wani mataki na soja da za a dauka a kan kokarin da suke yi na ceto kasarsu zai fuskanci martani mai kwari.

Mun yi takaicin yadda juyin mulki ke yaduwa a yankin Afrika ta yamma a daidai wannan lokacin da ake kokarin tabbatar da mulkin dimokradiyya a yankin, a kan haka muna masu shiga sahun al’ummar duniya na kira da a gaggauta dawo da mulkin dimokradiyya a Nijar da sauran kasashen da sojoji suka hambarar da zababbun shugabaninsu.

Muna kuma kira ga ECOWAS da sauran kungiyoyin duniya ciki har da Majalisar Dinkin Duniya da su yi taka-tsan-tsan wajen tafiyar da lamarin kasar Nijar don a kauce wa tashin hankali. Domin kuwa yekuwar yaki zai kara tagomashi da farin jinin sojojin kasar ne kawai wainda hakan zai kuma iya kaiwa ga tashin hankali a sassan kasar da ma wasu kasashe makota. Mun yi imanin cewa, tattauanwa da shugabanin masu juyin mulkin zai matukar taimakawa, ta yadda za su fito da tsari da jadawalin mayar da kasar tsarin mulkin dimokradiyya a nan gaba kadan.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Ba Zan yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ba, Cewar Dikko Radda

Next Post

Kamfanonin Da Suka Durkushe A Arewa Cikin Shekara 44

Related

NiMet Ta Yi Hasashen Cikin Watan Yulin 2025 Za A Tabka Ambaliyar Ruwan Sama A Jihohin Nijeriya 19
Da ɗumi-ɗuminsa

NiMet Ta Yi Hasashen Cikin Watan Yulin 2025 Za A Tabka Ambaliyar Ruwan Sama A Jihohin Nijeriya 19

10 hours ago
Shafin Yanar Gizo Na ADC Ya Tsaya Cak Saboda Ɗumbin Magoya Baya Masu Son Yin Rijista
Da ɗumi-ɗuminsa

Shafin Yanar Gizo Na ADC Ya Tsaya Cak Saboda Ɗumbin Magoya Baya Masu Son Yin Rijista

11 hours ago
Gwamna Peter Mbah Ya Ƙaddamar Da Jiragen Kasuwanci 3 Na ‘Enugu Air’ Mallakin Jihar
Da ɗumi-ɗuminsa

Gwamna Peter Mbah Ya Ƙaddamar Da Jiragen Kasuwanci 3 Na ‘Enugu Air’ Mallakin Jihar

12 hours ago
Kotu Ta Umarci Majalisar Dattijan Nijeriya Da Ta Gaggauta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Natasha
Da ɗumi-ɗuminsa

Lauyoyin Majalisar Dattawa Sun Ƙaryata Natasha Kan Cewa Kotu Ta Ce Ta Koma Bakin Aiki

14 hours ago
Namadi Sambo Ya Yaba Wa Gwamna Abba Yusuf Kan Bunƙasa Ɓangaren Ilimi Da Gine-Gine A Kano
Manyan Labarai

Namadi Sambo Ya Yaba Wa Gwamna Abba Yusuf Kan Bunƙasa Ɓangaren Ilimi Da Gine-Gine A Kano

15 hours ago
China Ta Mayar Da Martani Kan Barazanar Trump Na Ƙarin Haraji Ga Kasashen BRICS
Manyan Labarai

China Ta Mayar Da Martani Kan Barazanar Trump Na Ƙarin Haraji Ga Kasashen BRICS

17 hours ago
Next Post
‘Yan Takaran Gwamna 8 Sun Mara Wa Gwamnan Gombe Baya

Kamfanonin Da Suka Durkushe A Arewa Cikin Shekara 44

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-Ɗumi: Osimhen Ya Amince Da Komawa Galatasaray Na Dindindin

Da Ɗumi-Ɗumi: Osimhen Ya Amince Da Komawa Galatasaray Na Dindindin

July 7, 2025
Sin Za Ta Ci Gaba Da Karfafa Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Kan Tinkarar Sauyin Yanayi

Sin Za Ta Ci Gaba Da Karfafa Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Kan Tinkarar Sauyin Yanayi

July 7, 2025
Ƙungiyar Al’ummar Igbo Ta Ohanaeze Ndigbo Ta Ce Tinubu Ya Fi Ƙarfin ‘Yan Jam’iyyar Haɗaka Ta ADC

Ƙungiyar Al’ummar Igbo Ta Ohanaeze Ndigbo Ta Ce Tinubu Ya Fi Ƙarfin ‘Yan Jam’iyyar Haɗaka Ta ADC

July 7, 2025
Sin Za Ta Gina Wuraren Cajin Ababen Hawa Masu Ingantaccen Lantarki

Sin Za Ta Gina Wuraren Cajin Ababen Hawa Masu Ingantaccen Lantarki

July 7, 2025
NiMet Ta Yi Hasashen Cikin Watan Yulin 2025 Za A Tabka Ambaliyar Ruwan Sama A Jihohin Nijeriya 19

NiMet Ta Yi Hasashen Cikin Watan Yulin 2025 Za A Tabka Ambaliyar Ruwan Sama A Jihohin Nijeriya 19

July 7, 2025
Sin Ta Kafa Kungiyar Masana Masu Binciken Sararin Samaniya Mai Zurfi Ta Farko

Sin Ta Kafa Kungiyar Masana Masu Binciken Sararin Samaniya Mai Zurfi Ta Farko

July 7, 2025
Xi Ya Ajiye Furanni Ga Wadanda Suka Mutu Yayin Yakin Bijirewa Harin Japan

Xi Ya Ajiye Furanni Ga Wadanda Suka Mutu Yayin Yakin Bijirewa Harin Japan

July 7, 2025
Asibiti Mai Zaman Kansa A Kano Zai Fara Aikin Manyan Tiyatu Tare Da Rage Kuɗi Kaso 50%

Asibiti Mai Zaman Kansa A Kano Zai Fara Aikin Manyan Tiyatu Tare Da Rage Kuɗi Kaso 50%

July 7, 2025
Shafin Yanar Gizo Na ADC Ya Tsaya Cak Saboda Ɗumbin Magoya Baya Masu Son Yin Rijista

Shafin Yanar Gizo Na ADC Ya Tsaya Cak Saboda Ɗumbin Magoya Baya Masu Son Yin Rijista

July 7, 2025
Sin Na Bikin Cika Shekaru 88 Da Dukkan Al’ummar Kasar Ta Fara Yakin Kin Jinin Harin Sojojin Japan

Sin Na Bikin Cika Shekaru 88 Da Dukkan Al’ummar Kasar Ta Fara Yakin Kin Jinin Harin Sojojin Japan

July 7, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.