Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sanar da naɗin Muhammad Babaganaru a matsayin sabon kocinta kwanaki kaɗan bayan dakatar da kocinta, Evans Ogenyi da mataimakinsa Ahmed Garba Yaro Yaro.
Ƙungiyar ta kasa taɓukka abun a zo a gani a wannan kakar wasan ta shekarar 2025/26.
- ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa
- Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja
Ƙungiyar ta tabbatar da dawowar Babaganaru a wata sanarwa da ta fitar a hukumance a ranar Talata.
Ta bayyana cewa zai fara aiki nan take yayin da ƙungiyar Sai Masu Gida ke ƙoƙarin dawowa kan ganiyarta a gasar Firimiyar Nijeriya.
Sanarwar ta ce: “Hukumar gudanarwa ta Kano Pillars FC ta sanar da naɗin Muhammad Babaganaru a matsayin muƙaddashin mai ba ƙungiyar shawara kan fasaha, zai ci gaba da aiki nan take, muna yi wa koci Babaganaru fatan samun nasara a sabon muƙaminsa domin ya jagoranci ƙungiyar Sai Masu Gida a wasanni masu zuwa.”
Babaganaru, ya taɓa jagorantar ƙungiyar inda ya lashe kofunan gasar NPFL guda biyu a shekarun 2011/12 da 2012/13 a lokacin da ya yi aiki a baya.
Ana sa ran zai kawo gogewa da a wannan sabon babi na horar da ƙungiyar.
A halin yanzu Pillars tana matsayi na 18 a kan teburin gasar bayan wasanni takwas, inda ta samu nasara biyu kacal, ta yi canjaras biyu da kuma rashin nasara huɗu.