Kwanan baya, jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te ya gabatar da jawabai masu taken wai “jawabai 10 game da hadin kan al’umma”, da nufin ba da ingantacciyar hujja ga ra’ayinsa mai shirme game da ballewar Taiwan daga kasar Sin, tare da yaudarar jama’ar yankin da kuma yaudarar jama’ar duniya.
Ko Lai ya manta da cewa, a ran 19 ga watan Mayun da ya shude, shekaru 9 a jere ne babban taron hukumar lafiya ta duniya WHO ya ki yarda da shirin da wasu kasashe tsirraru suka gabatar na halartar Taiwan taron. Yawancin kasashen duniya sun nanata matsayinsu kan kiyaye kudurin babban taron MDD mai lamba 2758, da nace wa ga bin ka’idar kasar Sin daya tak a duniya, da kin yarda da halartar yankin Taiwan babban taron WHO, lamarin da ya shaida cewa, manufar kasar Sin daya tak a duniya ta samu amincewa daga al’ummun duniya.
Ya zuwa yanzu, adadin kasashen da suka kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin ya kai 183, kuma dukkansu sun nace ga bin manufar kasar Sin daya tak a duniya, inda wasu suka bayyana a fili rashin jin dadinsu game da yunkurin ballewar yankin Taiwan daga kasar Sin da kuma goyon bayan dinkewar kasar baki daya. Matakin da ya bayyana cewa, al’ummun duniya sun kai ga matsaya daya kan wannan batu har ya zama ka’idar huldar kasa da kasa.
Idan muka duba sakamakon binciken jin ra’ayin jama’a da jaridar Formosa Post ta yankin Taiwan ta gudanar, tuni gamsuwar jama’ar yanki game da ayyukan da Lai Ching-te ya yi, ta ragu zuwa kashi 44.7%, adadin da ya kai matsayi mafi kankanta tun bayan da ya hau kujerar mukaminsa a watan Mayun bara. Kowa ya san yankin Taiwan wani bangare ne da ba za a iya ware shi daga kasar Sin ba, kuma wannan shi ne matsaya daya da al’ummun Sinawa da yawansu ya kai biliyan 1.4 ciki hadda jama’ar yankin Taiwan da yawansu ya kai miliyan 23 suka dauka, wanda kuma ra’ayi daya ne da kasa da kasa suka cimma. Maganar Lai kamar tururuwa ne a gaban giwa, za a taka ta ta mutu, abin da zai kawo karshen ra’ayin baraka. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp