Yau Talata, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai.
A yayin taron, mataimakin shugaban babban bankin kasar Sin Xuan Changneng ya bayyana cewa, an samu habakar amfani da kudin Yuan na kasar Sin RMB a tsakanin kasa da kasa a shekarun nan.
- Huldar Sin Da Afirka Za Ta Zama Abin Koyi Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya Ta Daukacin Bil’adama
- Xi Ya Zanta Da Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Ta Tarho
A fannin biyan kudi, RMB ya riga ya zama kudi na hudu mafi karbuwa wajen biya a duniya kwanan nan.
Haka nan, a fannin tattara jari, kudin Yuan na kasar Sin ya zama daya daga cikin manyan kudade guda uku a cikin harkokin cinikayya a duniya. A shekarar 2024, takardun bashin Panda da hukumomin hada-hadar kudi da kamfanonin kasashen waje suka wallafa, sun kai kusan yuan biliyan 200, wadanda suka karu da kashi 32 cikin dari bisa makamancin lokacin na shekarar 2023.
A fannin adana kudi, manyan bankuna ko hukumomin dake kula da kudade fiye da 80 na kasashen waje sun dauki kudin Yuan na kasar Sin a matsayin ma’aunin musayar kudaden da aka adana. (Safiyah Ma)