A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da shugaban majalisar tarayyar Turai Antonio Costa ta wayar tarho bisa muradin haka da Antonion ya nuna.
A yayin zantawar, shugaba Xi ya bayyana cewa, a ko yaushe kasar Sin tana amanna da yankin Turai a matsayin ginshiki mai muhimmanci a bangaren samar da hadin kan kasashen duniya da kuma nuna goyon baya ga hadewar yankin da kuma dabarun cin gashin kai na tarayyar Turai.
- Hare-haren ‘Yan Bindiga Sun Ragu A Watan Disamban 2024, Amma Har Yanzu Ana Fuskantar Barazana – Rahoto
- Sojoji Sun Fara Binciken Kuskuren Kashe Fararen Hula Da ‘Yan Sa-kai A Zamfara
Bugu da kari, shugaban na Sin ya ce, duk runtsin da za a shiga a huldar kasashen duniya, kamata ya yi kasar Sin da tarayyar Turai su ci gaba da kiyaye kyakkyawar aniyarsu ta kyautata huldar diflomasiyya, da karfafa sadarwa a tsakaninsu da kuma bin matakan kawance sau da kafa.
A nashi bangaren, Antonio Costa ya bayyana cewa, zamanin da ake ciki yanzu a cike yake da dimbin kalubale, kuma duniya tana bukatar Turai da kasar Sin su kara yin hadin gwiwa wajen fuskantar kalubalen da ke shafar daukacin duniya irin su sauyin yanayi, tare da bayar da kyakkyawar gudummawa ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ci gaban duniya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)