Babban bankin kasar Sin ya yi alkawarin kara aiwatar da matsakaicin tsarin hada-hadar kudi da kuma karfafa goyon baya ga kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da sayayya a rabi na biyu na shekarar nan.
Bankin na jama’ar kasar Sin (PBOC) ya bayyana cewa, tallafin kudi da ake bayarwa don bunkasa tattalin arziki, da sauye-sauyen ginshikai, da samun ci gaba mai inganci ya karu tun daga farkon shekarar 2025, a yayin taronsa da ya gudanar na tsakiyar shekara.
- An Dawo Da Wutar Lantarki A Dukkan Kauyukan Da Aka Tafka Ruwa Da Iska A Beijing
- An Dawo Da Wutar Lantarki A Dukkan Kauyukan Da Aka Tafka Ruwa Da Iska A Beijing
Zuwa karshen watan Yuni, rancen da aka bayar a fannin fasaha ya karu da kashi 12.5 cikin dari, na bangaren samar da ci gaba mara gurbata muhalli kuma ya karu da kashi 25.5, yayin da kuma na kula da tsofaffi ya karu da kashi 43 bisa dari, dukkansu a mizanin shekara-shekara.
Babban bankin na PBOC ya ce ya himmatu wajen habaka samun lamuni ga kanana da matsakaitan masana’antun kimiyya da fasaha, a kokarin da ake yi na tallafa wa bunkasa masana’antu.
A halin da ake ciki kuma, babban bankin kasar zai kara dagewa wajen bunkasa zuba jari da samar da kudade a bangaren hada-hada tsakanin kasa da kasa, yayin da kuma zai kara kokarin inganta gine-gine da kayayyakin aiki na manhajar kudin kasar Sin RMB na zamani. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp