Babban bankin kasar Sin zai aiwatar da jerin matakai da za su inganta hidimomin hada hadar kudi da nufin habaka yin amfani da kudi ga masu sayayya, a cewar wani rahoto da babban bankin kasar (PBOC) ya fitar a yau Juma’a.
Bisa ga rahoton manufofin hada hadar kudi na rubu’in farko na shekarar 2025 na PBOC, bankin zai fi mai da hankali wajen aiwatar da manufar hada hadar kudi mai sassauci. A lokaci guda kuma, zai yi amfani da tsarin bayar da lamuni da sarrafa takardun lamuni, wanda za a yi amfani da shi wajen jagorantar cibiyoyin hada hadar kudi don kyautata ba da goyon baya ga masu amfani da kudi a manyan sassa, kamar yawon shakatawa, abinci, nishadi da ilimi. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)