Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi bayani game da wayewar da ci gaban hadin gwiwar kasashen Sin da Amurka ya kawo. Yana mai bayyana cewa, zaman lafiya shi ne babban ginshikin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Wang ya bayyana hakan ne a yayin wata liyafa da aka shirya, albarkacin bikin cika shekaru 45 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Amurka a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
- Ana Maraba Da Karin Abokai Da Su Ziyarci Xinjiang
- Sin Ta Zamo Ta Daya A Yawan Rajistar Kamfanonin Sarrafa Farantan Samar Da Lantarki Ta Hasken Rana
Wang ya ce, hadin gwiwar kasashen biyu ta fuskanci kwan-gaba-kwan-baya, wanda ya kawo wasu darussa masu muhimmanci, ya kara da cewa, ba a fuskanci wani rikici ko fada tsakanin manyan kasashen biyu ba, wannan shi kansa, wani muhimmin abu ne ga zaman lafiyar daukacin bil Adama
Wang Yi ya bayyana cewa, hadin gwiwa shi ne zabi mafi dacewa ga kasashen Sin da Amurka wajen daidaita tsakaninsu, ya ce hadin gwiwar samun nasara tare, shi ne mafi muhimmanci ga kasashen biyu.
Wang ya kuma gabatar da shawarwari da dama kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a San Francisco na kasar Amurka.
Ya kuma yi kira ga bangarorin biyu, da su kasance masu mutunta juna, da kara fahimtar juna ba tare da bata lokaci ba, yana mai jaddada cewa, kasar Sin ba ta da niyyar maye gurbi ko kawar da wani, balle neman yin babakere. Kasar Sin ta kuduri aniyar gina alakar Sin da Amurka mai karko, lafiya da dorewa bisa mutunta juna.
A jawabinsa yayin liyafar, jami’in hulda da jama’a na ofishin jakadancin Amurka dake kasar Sin, David Meale, ya bayyana cewa, a madadin bangaren Amurka, yana taya kasashen biyu murnar cika shekaru 45 da kulla huldar diplomasiyya, yana mai cewa, bangaren Amurka na son aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da sa kaimi ga raya hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim)