Abubuwan Da Ake Bukata
- Shinkafar tuwa
- Yis
- Bakar hoda (Baking powder)
- Sikari
Yadda Ake Sarrafawa
Za a jika shinkafar tuwo a wanke ta tas, a markada, idan an markada, sai a zuba yis kadan da bakar hoda a kai shi rana ya tashi.
Sai a dora kaskon suyar sunasir a wuta, idan ya yi zafi sai ana shafa mai kadan a kaskon ana diban kullun ana zubawa kamar wainar fulawa, ana rufewa har sai ya yi.
Aci dadi lafiya.
Talla