Fiye da shekaru goma da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dora samun ci gaba marar gurbata muhalli a matsayin wata muhimmiyar manufar raya kasa. Ya taba fitar da manufar raya kasa ta hanyar bayar da muhimmnci ga “Muhalli”, wadda ta yi nuni da cewa ingantaccen yanayin muhalli abu ne mai matukar daraja don samun ci gaba. Tun daga wannan lokacin, kasar Sin ta ci gaba da yin sauye-sauye masu kiyaye muhalli, inda ta zama kasa mafi girma a duniya wajen kera batir na lithium da motocin masu amfani da lantarki.
Game da hakan, a yayin da ake tattaunawa da Jorge Moreira da Silvas, babban darektan ofishin kula da ayyuka na MDD, a wani shiri mai suna “Leaders Talk” da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya gabatar a birnin Beijing, ya bayyana cewa, kokarin da kasar Sin ta yi da kuma sakamakon da ta samu wajen samar da makamashin da ake sabuntawa, da samun ci gaba mai dorewa, sun nuna wata alama mai kyau kuma mai inganci. Kuma wannan na da matukar alfanu ga batun dakile sauyin yanayin duniya.
Bugu da kari, Jorge Moreira da Silvas ya ce, ya yaba da hangen nesa da aniyar aiwatarwar da shugaba Xi Jinping ya nuna a fannin dakile sauyin yanayi da samun ci gaba mai dorewa. Gagarumin ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin tattalin arzikin mai kiyaye muhalli, musamman a fannin makamashin da ake sabuntawa da kuma sufurin ababen hawa masu amfani da wutar lantarki, ba wai kawai yana da muhimmanci sosai ga ita kanta kasar Sin ba ne, har ma ga duk fadin duniya.
A sa’i daya kuma, kasar Sin tana goyon bayan ra’ayin damawa da bangarori daban-daban, kuma tana taka rawa sosai a cikin ajandar samun ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030, da kuma ajandar dakile sauyin yanayi ta duniya. Kazalika, ya ce ya yi imani da gaske cewa, kasar Sin za ta cimma burin samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za ta fitar, da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin kafin shekarar 2060. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp