Babban Jami’in yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a birnin tarayya Abuja (FCT), Danladi Etsu Zhin, ya rasu yana da shekaru 54 a duniya bayan gajeruwar rashin lafiya.
Wani makusancin marigayin, Godwin Omonya, wanda ya tabbatar wa manema labarai rasuwar, ya ce Zhin, wanda tsohon shugaban karamar hukumar Kuje ne da ke babban birnin tarayya Abuja, ya rasu ne da sanyin safiyar Lahadi, a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja.
- Zan Sayar Da Matatun Mai Ga ‘Yan Kasuwa Idan Aka Zabe Ni – Atiku
- Jam’iyyar PDP A Kebbi Ta Shirya Tarbar Dan Takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar
Omonya, wanda kuma shi ne mai ba tsohon shugaban shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, ya ce, Zhin, ya shafe sama da wata guda yana kwance a asibiti sakamakon rashin lafiya kuma ya rasu da sanyin safiyar Lahadi.
A cewarsa, Marigayi Zhin ya kasance dan takarar majalisar wakilai a mazabar Abuja ta Kudu a karkashin jam’iyyar APC, a zaben 2019.
Marigayin, wanda ya rike matsayin shugaban karamar hukumar Kuje karo biyu, ya auri Paulina Etsu Zhin, wadda suke da yara maza uku da mata biyu.