Babban layin samar da wutar lantarki ga al’umma a Nijeriya wato ‘National Grid’ a daren ranar Litinin ya lalace, inda ya jefa al’ummar kasar cikin duhu na rashin wuta, bayan sake gyara shi na ‘yan dakika a ranar Talata, kasa da awa 24 nan ma ya sake lalacewa, hakan ya zama layin ya lalace sau 7 a cikin shekarar 2024.Â
Kamfanonin rarraba wutar lantarki (DISCOS) su ne suka sanar da lalacewa babban layin samar da wutar lantarki a daren ranar Litinin.
- MOFA: Ministan Harkokin Wajen Birtaniya Zai Ziyarci Kasar Sin
- Ɗaliban Kwalejin Kimiyya Ta Jega Sun Yi Zanga-Zanga Har Da Ƙone-Ƙone
Daya daga cikin kamfanonin ya shaida cewa babban layin lantarkin ya lalace zuwa 0.00GW wajajen karfe 6:30 na yammacin ranar Litinin.
Kamfanin raba wutar lantarki na Inugu (EEDC) ya shaida wa kwastomominsa cewa sakamakon lalacewar babban layin wutar dukkanin wadanda suke samun wuta ta hannunsa ba za su samu ba a daidai wannan lokacin.
“Saboda haka, kan wannan lamarin, dukkannin tashoshinmu na TCN ba su samun wuta ba, don haka ba za mu samu damar rabar da wuta ga kwastomominmu da suke jihohin Abiya, Anambra, Ebonyi, Inugu, da Imo ba.
“Muna zaman jiran karin haske da cikakken bayani kan lalacewar wutar da kuma batun dawowar wutar daga cibiyar kula da wutar ta kasa (NCC).”
Kazalika, ita ma kamfanin rarraba wutar lantarki ta Abuja (AEDC) ta ce, “Ya ku kwastomominmu masu daraja, ku dan yi hakuri an fuskanci katsewar wutar lantarki sakamakon akasin da aka samu daga babban layin wutar lantarki ta kasa da karfe 6:58 na daren ranar Litinin, wannan ya shafi rabar da wuta da muke yi a yankunan da suke samun wuta daga garemu.
“Muna masu bayar da tabbacin cewa muna aiki tukuru da masu ruwa da tsaki wajen ganin an gyara wuyar nan ba da jimawa ba da zarar komai ya daidaita daga babban layin wutar. Mun gode da fahimtarmu.”
Tuni dai hukumar da ke kula da wutar lantarki a Nijeriya ta bayar da tabbacin cewa an dukufa wajen gyara wutan ta yadda ba za a sake samun jinkiri ba. Sun bai wa jama’a hakuri bisa dan karamin katsewar wutar da aka samu.