A jiya ne, babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin, Wang Huning, ya gana da manyan mambobin kungiyar Musulmai ta kasar, inda ya taya su murnar cika shekaru 70 da kafuwar kungiyar.
Mamban zaunannen kwamitin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), kana shugaban kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Wang, ya gana da mambobin ne, a yayin wani taro da aka gudanar a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, domin tunawa da zagayowar ranar da kungiyar ta cika shekaru 70 da kafuwa, inda ya mika sakon gaisuwa ga mabiya addinin Musulunci da dukkan Musulman kasar Sin.
Wang ya kuma yabawa aikin da kungiyar ke yi, wajen jagorantar al’ummar Musulmi wajen bin hanyar da ta dace da zamantakewar gurguzu da kuma taka rawar gani a kokarin zamanantar da tsarin gurguzu. Ya kara da cewa, kungiyar ta bayar da gudunmawa a zahiri da karfinta domin ci gaban kasa da farfadowar kasa.
Don haka, Wang ya yi kira ga al’ummar Musulmin kasar Sin, da su gudanar da kyakkyawar al’ada ta nuna kishin kasa, da nuna goyon baya ga JKS da tsarin gurguzu mai sigar kasar Sin. (Ibrahim)