Yayin ziyararsa kasar Sin kwanan nan, babban mashawarcin gwammatin wucin-gadi ta kasar Bangladesh, Muhammad Yunus, ya tattauna da wakiliyar CMG, wato babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, inda a cewarsa, a matsayin kasa ta farko a kudancin nahiyar Asiya, wadda ta rattaba hannu tare da kasar Sin kan takardar bayanin hadin-gwiwa game da raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, Bangladesh na matukar bukatar shawarar nan, ganin yadda aikin raya shawarar ke da muhimmanci sosai.
Muhammad Yunus ya ce, Bangladesh na matukar bukatar cudanyar sassa daban-daban. Hanyoyin mota na taka rawar gani wajen jigilar hajoji, don haka kasar na bukatar kara shimfida hanyoyin mota. Hanyoyi su ne tamkar manyan jijiyoyin tattalin arzikin kasa, shi ya sa ya kamata a raya tattalin arziki yadda ya kamata bisa tushen tsarin jigilar hajoji ta hanyoyin mota. Sabili da haka, raya shawarar “ziri daya da hanya daya” cikin hadin-gwiwa na taka muhimmiyar rawa, ganin yadda al’ummar da abun ya shafa za su iya cin gajiya daga haka. Darajar tsarin ba ta tsaya kan hada mafari da karshe ba, har ma za su sa ko wane sashi da ya shafa ya samu alfanu. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp