Babban taron Kamfanin Jaridun LEADERSHIP karo na 16, ya zauklo yadda za a ceto Nijeriya daga matsalolin da suka yi wa kasar katutu ta fuskar tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma yayin da masana, shugabanni daga bangarori daban-daban suka gudanar da jawabai.
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Farfesa Kingsley Moghalu, ya bayyana cewa, matsalar tattalin arzikin da Nijeriya ta samu kanta a ciki wadda ta haifar da hauhawar farashin kayan masarufi da kuma tsadar rayuwa da kuma karyewar darajar naira za ta ci gaba da hauhawa har sai gwamnati ta shirya daukar mataki masu tsauri don kawo karshen matsalolin.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Kara Gina Madatsun Ruwa Domin Noman Rani
- Binciken CGTN: Sama Da Kashi 80% Na Masu Amsa Tambayoyi A Duniya Sun Yaba Da Manufar Harkokin Waje Na Sin
Ya kuma alakanta matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu a kan cin hanci da almundahana da aka tafka a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Farfesa Moghalu ya kara da cewa, a kokarin Shugaban Kasa Bola Tinubu na shawo kan matsalar tattalin arzikin kasa ya yi wasu manyan kura-kurai a watanninsa 7 na farkon mulkinsa wadanda suka kara tabarbarewar matsalar da ake fuskanta a yanzu.
Ya ce, janye tallafin man fetur da rashin dakatar da karyewar darajar Naira da gwammnatin ta yi ba tare da ta shirya yadda za ta fuskanci sakamakon da za su fito ba ya taimaka jefa ‘yan Nijeriya shiga halin ni’yasu.
A kan haka, tsohon mataimakin shugaban CBN ya ce, ya kamata Shugaban Kasa Tinubu ya yi wa gwamnatinsa garanbawul musamman masu rike da mukamai, tun daga ministoci da sauran masu bashi shawara tun kafin gwamnatin ta cika shekara 1 a kan karagar mulki. Ya kuma kara da cewa, masu tafiyar da harkokin mulkiin a halin yanzu ba su da cikakken kwarewar da zai kai kasar nan ga tudun muntsira.
Ya kuma shawarci shugaban kasa da ya kafa kwamitin kwararru na mutum 7 da za su jagoranci fitar da kasar nan daga halin da take ciki.
Tattalin Arzikin Nijeriya Ba Ya Cikin Garari – Tinubu
A nasa martanin, shugaban kasa Tinubu ya yi watsi da masu cewa, tattalin arzikin kasar nan na cikin garari, ya kuma bayyana irin nasarorin da aka samu a kokarin bunkasa tattalin arzikn Nijeriya.
A jawabInsa bayan karramawar da aka yi masa a matsayin Gwarzon LEADERSHIP a 2023, ya ce, bai kamata a rika kwatanta tattalin arzikin Nijeriya a matsayin yana cikin garari ba.
Shugaban kasar wanda Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris, ya wakilta, ya amince da cewa, lallai Nijeriya na fuskantar manyan kalubale a halijh yanzu amma ana kokarin ganin an gyara kurakuran da aka tafka a baya.
Ya kuma mika godiyarsa ga shugabanin da dukkan ma’aikatan LEADERSHIP a bisa karramawar da aka yi masa, ya ce, tabbas wannan karramarwar za ta taimaka masa wajen ganin ya kara kwazo a kokarisan na kai kasar nan tudun-mun tsira.
Shugaban kasa Tinubu ya kuma yi jijina ga marigayi shugaban kamfanin jarifar LEASERSHIP Sam Nda-Ishiah da ya kirkiro da kamfanin ya kuma yaba da yadda uwargidansa, Misis Nda-Ishaiah, ta jajirce wajen ganin kamfanin ya ci gaba da bunkasa duk kuwa da kalubalen tattalin arzikin da ake fuskanta.
Karramawar Za Ta Kara Karfafa Mu – Gwamnoni
Haka kuma, a nasa jawabin Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Bago wanda ya yi jawabi a madadin gwamnonin da aka karrama a matsayin Gwarazan Gwamnoni na 2023, ya ce, karramarwa za ta kara karfafa su wajen yi wa al’umma ayyukanm bunkasa rayuwa.
A banbaren samar da abinci ya ce, gwamnatinsa za ta noma miliyoyin hektar don samar da abincin da za a yi amfani da shi a ciki da wajen kasar nan.
A nasa jawabin, dan takara shugabancin kasa a jam’iyyar LP, Mista Peter Obi, abin kunya ne a ce kasar Yukrain da ke cikin yaki za ta tallafa wa Nijeriya da abinci bayan Jihar Neja kawai na ikon ciyar da Afirika gaba daya. Ya kuma danganta halin matsin rayuwa da talaucin da ake fuskanta da matsalar tsaro a kasar nan, ya ce, in har aka samu nasarar maganin matsalar tsaro to lallai an yi maganin yunwa don manoma da dama sun yi watsi da filayen noma saboda matsalar tsaro da ayyukan ‘yan ta’adda.
Tunda farko, shugabar kamfanin LEADERSHIP media group, Zainab Nda-Isaiah, ta ce, karramarwa na LEADERSHIP an ba mutane ne da suka yi fice a bangarorin rayuwa daban-daban. Ta ce, muna amfani da wannan taron na karramwar ne don foti da muaten da suka yi fice a fannonin raywua daban don su zama abin koyi ga sauran al’umma musamman matasa masu tasowa.
Ta kuma yi jijina ga maigidanta marigayi Sam Nda-Isaiah, wanda kirkiro da kamfanin jaridar LEADERSHIP, ta ce, mutum ne mai hangen nesa wanda ya yi kishin Nijeriya ya kuma yi amfani da alkalaminsa wajen samar da ci gaba a kasa, ta kuma mika godiyarta ga dukkan wadanda suka bayar da gudummwar ganin an samu nasarar wannan taron musamman shugaban kasa Bola Tinubu, da tsohon mataimakin gwamnan Babbann Bankin Nijeriya Farfesa Kingsley Moghalu, da kuma Etsu Nupe, Dakta Yahaya Abubakar.
Shi ma da yake tsokaci, bayan ya karbi lambar karramarwar da aka yi wa Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu, OFR, wanda aka ba shi lambar Gwarzon Kyautata Walwalar Jama’a, Wazirin Bauchi, Muhammad Uba Ahmed Kari, ya ce, Sarkin ya so ya halarci taron da kansa amma saboda wasu matsaloli da sujka sha kansa ya sa bai samu daman zuwa, amma ya matukar mutunta karramawa da aka yi masa zai kuma karfafa masa wajen kara kaimi wajen ayyukan bunkasa rayuwar al’umma a duk inda ya samu kansa.
Da yake jawabin godiya, mataimakin shugaban kamfanin LEADERSAHIP, Mista Azu Ishiekwene, ya yaba wa wadanda suka samu daman halartar bikin ne, ya ce, irin wannan gudummawar yana kara karfafa musu gwiwa wajen kara ayyukan ci gaban al’umma kamar yadda wanda ya kirkiro da kamfanin, Sam ya assasa.