ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Yanka Ta Tashi: Jami’ar Modibbo Adama Ta Kori Dalibi, Ministan Ilimi Ya Ce Bai Koru Ba

by Muh'd Shafi'u Saleh
2 years ago
Modibbo Adama

Hukumar gudanarwar jami’ar Modibbo Adama, da ke Yola, ta kori wani dalibinta mai suna Salihu Usman da ya fito daga yankin karamar hukumar Ganye a jihar Adamawa.

Salihu Usman da yake zangon karatu na biyu, jami’ar ta ce ta gano cewa ya shigo ne da takardar jarrabawa ta NBAIS, wato shaidar Hukumar Jarrabwa ta Nazarin Larabci da Ilimin Islama.

  • An Rufe Taron Koli Na Kafofin Yada Labarai Dangane Da Kwaikwayon Hazikancin Dan Adam A Afrika
  • Kano Za Ta Haɗa Gwiwa Da Afrinvest Don Haɓɓaka Kasuwanci Da Ci Gaban Jihar 

Rahotanni sun nunar da cewa, Jami’ar Modibbo Adama, Yola, ba ta tashi gano hakan ba, sai da Salihu Usman ya kai zangon karatu na biyu, yayin da ya yi wa ‘yan ajinsu fintinkau a jarrabawarsu ta zangon farko da ta biyu.

ADVERTISEMENT

Bayanan sakamakon jarrabawar Salihu sun nuna ya samu maki a ma’aunin karatu na jami’a da CGPA 4.47, a jarabawar zangon farko, ya kuma samu 4.18 a zangon jarrabawa na biyu.

An kori Salihu Usman ne biyo bayan kafa kwamitin tantance takardunsa da jami’ar ta yi inda kwamitin ya tabbatar da cewa da takardun jarrabawar NBAIS, ya shigo jami’ar.

LABARAI MASU NASABA

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

Binciken wakilinmu ya gano cewa Salihu Usman ya yi jarrabawar JAMB ta kasa wacce ake yi da Turanci, ya samu makin da Jami’ar Modibbo Adama take bukata kuma aka dauke shi domin yin karatun Digiri. Sai dai hakan bai sa kwamitin la’akari da kwazon da Salihu Usman ya nuna a jarrabawa ba, ya bayar da shawarar korar shi.

A ranar 13 ga Disimbar 2023, hukumar jami’ar ta ba shi takardar kora mai lamba MEU/R/ACA/S.5/BOL.1, wacce Malama A.K. Mohammed, ya rattaba wa hannu a madadin magatakardar jami’ar.

Salihu Usman dai ya yi karatunsa ne a cibiyar Nazarin Larabci da Ilimin Addini ta ‘Atiku Abubakar Center for Arabic and Islamic Studies’ da ke Ganye, a Karamar Hukumar Ganye a Jihar Adamawa, kuma a makarantar ya yi jarrabawar NBAIS da JAMB. Ganin kwazonsa, ya sa shugaban makarantar, Malam Kabiru Sa’ad, ya sanar da Malam Muhammadu Sani Jada wanda daya ne daga cikin jiga-jigan kafa makaratun cibiyar ta Atiku da ke Ganye, Jada, Toungo da Kojoli fiye da shekaru ashirin, halin da ake ciki.

Malam Sani Jada bai yi kasa a gwiwa ba, ya karbi takardun Salihu Usman ya rubuta wa NBAIS wacce ke da hidikwata a Kaduna, kuma ya yi tattaki ya je Kaduna, ya fargar da shugabannin NBAIS hadarin da ke tattare da nuna halin ko oho da rashin daukar daliban da suka zana jarrabawar NBAIS da jami’o’in Nijeriya musamman ma dai ga Jami’ar Modibbo Adama Yola ta kori wanda JAMB ta dauka bayan har ya fara karatu.

Malam Sani Jada ya kara shaida wa NBAIS cewa, idan aka kyale wannan halin ya ci gaba; to kuwa dalibai za su kaurace wa jarabawar NBAIS baki-daya a Nijeriya, wanda kuma hakan ya tabbatar da nuna cewa, NBAIS ta kama hanyar mutuwa kenan kacokan.

Takardar da Malam Sani Jada ya rubuta wa NBAIS, ya kuma aike wa Ministan Ilmi; Farfesa Tahir Mammam (SAN) da kuma Hukumar Gudanar da Jami’o’i ta kasa (NUC) da ke Abuja.

Tuni dai Ministan Ilimin ya umarci Jami’ar Modibbo Adama Yola da ta rubuta wa Malam Muhammadu Sani Jada cikakken bayanin dalilin korar Salihu Usman daga jami’ar, bayan da jami’ar ta rubutu bayanin ne ta ce wai “ta dauki Salihu Usman ne bisa kuskure” (ERROR).

A wasikar martinin da Malam Muhammadu Sani Jada ya yi wa jami’ar ta Modibbo Adama, ya bayyana mamakin yadda jami’a za ta dauki dalibi bisa kuskure, ya ce dalibi ya yi rigista ta shiga ajin farko bisa kuskure, ya biya duk kudaden da jami’ar ta ayyana bisa kuskure, ya shiga aji har na tsawon zangon karatun farko bisa kuskure, ya yi jarrabarwar farko bisa kuskure, ya samu makin CGPA 4.47 duk ba’agano kuskuren ba.

Ya kara da cewa, dalibi ya sake dawowa zango na biyu ya yi rigista ya biya duk kudaden da jami’a ta ayyana domin karatun zangonsa na biyu, ya shiga aji ya yi jarabawar zango na biyu; har ya sake yi wa ‘yan ajinsu fintikau da makin CGPA 4.18 duk dai bisa kuskure, sannan aka gano cewa; wai Salihu Usman bai cancanta ya yi karatu a jami’ar ba.

Saboda haka, sai aka nada masa kwamitin da ya bayar da shawarar a kore shi, aka kuma kore shin daga jami’ar, ya ce indai haka ne wannan kuskure ya wuce kuskure; ya kai ga zama ganganci da rashin sanin makamar aiki.

Ya kara da cewa, indai har jami’a za ta dauki dalibi ta binciki takardunsa ta amince masa ya rika shiga aji har na tsawon zangon karatu (first semester) ya kuma yi jarrabawar wannan zangon karatu; ya samu CGPA 4.47, ya sake dawowa ya yi rigistar zango na biyu (second semester), sai sannan ne jami’a za ta gano dalibin ya shigo ne da takardun NBAIS, don haka ta kore shi; a kuma aiwatar da korar a ranar 13 ga watan Disamba, 2023, lallai kuwa akwai lauje cikin nadi.

Masu lura da abin da kaje ya dawo sun nuna cewa, ko shakka babu wannan kora akwai walakin Goro a Miya, bayan samun takarda da Malam Muhammdu Sani Jada ya yi, ya tura wa Ministan Ilmi Farfeso Tahir Mammam (SAN), inda ya umarci hukumar jami’o’i ta kasa (NUC) ta rubuta wa daukacin jami’o’in Nijeriya wasika kan cewa, jarrabawar NBAIS ingantacciyar jarrabawa ce, sannan kuma ta na da daraja kai daya da ‘O’ lebel’, kuma za ta bai wa duk wani dan Nijeriya damar shiga kowace irin jami’a.

Daga bisani, ofishin Ministan Ilmi Farfesa Tahir Mammam (SAN), a ranar 26 ga watan Fabrairun 2024; ta rubuta wa Shugaban Jami’ar Modibbo Adama Yola, takarda mai lamba FME/TE/SU/55A/T3/296, inda ta umarci jami’ar da ta janye takardar korar Salihu Usman tare da mayar da shi jami’ar, domin ci gaba da karatunsa nan take.

Umarni na biyu kuma shi ne, sauran daliban da Hukumar JAMB ta bai wa takardun amincewa, har ta ba su gurbin karatu da jami’ar Modibbo Adama Yola ta hana su; da ta tabbatar ta nemo su ta ba su guraben karatu ba tare da wani baba lokaci ba.

Binciken wakilinmu ya tabbatar da cewa, jama’ar yankin Kasar Ganye da kuma dukkanin Makarantun da ke mu’amala ta jarrabawa da NBAIS, sun yi matukar murna da farin ciki tare da jinjina wa Ministan ilimi; Farfesa Tahir Mammam (SAN), dangane da namijin kokarin da ya nuna a matsayinsa na Ministan Ilmin Nijeriya, domin kuwa matakin da ya dauka ya nuna za a kare hakkin dan talaka, domin shi ma ya samu damar yin karatu a manyan makarantun kasa.

A lokacin da wakilinmu ya samu ganawa da Salihu Usman, dalibin da Jami’ar ta Modibbo Adama Yola ta kora, cewa ya yi; jami’ar ta mayar da shi nan take, ya kara da cewa; jami’ar ta rubuto masa da takarda mai lamba MAU/R/ACA/S.5/BOI.1, a ranar 27 ga Fabrairun 2024 tare da sa hannun A.K Mohammed, wacce ke nuni da janye waccan kora da ta yi masa.

Da wakilinmu ya tuntubi Malam Muhammadu Sani Jada, kan batun cewa ya yi, “na gode wa Allah da ya taimake ni ya kuma ba ni ikon jajircewa da nema wa wannan dalibi dan talaka mai hazaka Salihu Usman ‘yancinsa na komawa makaranta don ci gaba da karatu.

“Ina kira ga Shugabanin Jami’ar Modibbo Adama Yola, da su rika yin adalci tare da samar da sashin da zai rika bai wa dalibai shawara, kan kwasa-kwasan da su ke son yin karantu a kansa, tun lokacin da dalibi ya shiga jami’ar, ba sai lokacin da yaro ya fara karatu ya wahala, iyayensa su ma suka wahala; sannan kuma sai a ce wai an sami kuskure (ERROR) a kore shi daga jami’a ba”, in ji Jada.

Al’ummar Masarautar Ganye, sun yi Allah san barka da wannan yunkurin da dansu Muhammadu Sani Jada ya yi, domin ya ceto dansu daga zama guda cikin zauna-gari-banza.

Yanzu haka dai, ya tabbata cewa Cibiyar Jarrabawar NBAIS; na daya daga cikin cibiyoyin zana jarrabawar shiga jami’o’i da sauran manyan makaratun Nijeriya.

Binciken LEADERSHIP HAUSA ya gano cewa, iyayen Salihu Usman, sai da suka sayar da gonarsu ta gado, kafin su kai ga samun damar biya wa dan nasu kudin shiga wannan jami’a ta Modibbo Adama da ke Yola.

A zantawarsa da wakilinmu, wani mazaunin yankin ya bayyana cewa, “ga wadanda suka san Malam Muhammadu Sani Jada, ba za su yi mamakin tsayuwar dakar da ya yi na ceto Salihu Usman daga kuskuren da Jami’ar Modibbo Adama ta yi ba, domin kuwa tun a shekarar 1990 Malam Muhammadu Sani Jada ya rike matsayin Shugaban Sashin Koyar da Malanta (Dean of school of education),na babbar Kwalejin Tarayya da ke Yola (FCE).

“Ya kuma ya ye dubban dalibai a matakin NCE, ya kuma yi ritaya tare da ajiye aikin koyarwa a shekarar 2023, ya na matsayin shugaban sashin koyar da ilmin kula da koyar da Jarirai da yara kanana (Dean School for Early Childhood education) na FCE, Yola.

“Daga nan ne kuma ya tsaya takarar kujerar Sanata a jam’iyyar APC, domin wakiltar Adamawa ta kudu, amma Allah bai ba shi nasara ba, sannan ya kuma rike mukamai da dama; ciki har da Shugabancin Karamar Hukumar Jada, a zamanin marigayi Janar Sani Abacha daga1994 zuwa 1996.

“Ya kuma shugabanci hukumar koyar da sana’o’in dogaro da kai; karkashin Hukumar LAS (Local Apprenticeship scheme) wanda Gwamnatin Baba mai Mangoro Hammanyero Nyako ta ba shi, hukumar da ta yi fice wajen taimaka wa matasa maza da mata; domin dogaro da kawunansu.” In ji shi.

Modibbo Adama
Muh'd Shafi'u Saleh
+ postsBio
  • Muh'd Shafi'u Saleh
    https://hausa.leadership.ng/author/muhd-shafiu-saleh/
    Jami’in Tsaro Ya Mayar da Dala 505 Da Riyal 30 Da Ya Tsinta A Yola
  • Muh'd Shafi'u Saleh
    https://hausa.leadership.ng/author/muhd-shafiu-saleh/
    Shahararren Malamin Addinin Islama A Adamawa Sheikh Ibrahim Abubakar Daware Ya Rasu
  • Muh'd Shafi'u Saleh
    https://hausa.leadership.ng/author/muhd-shafiu-saleh/
    An Yi Wa ‘Yansanda 110 Ƙarin Girma A Adamawa
  • Muh'd Shafi'u Saleh
    https://hausa.leadership.ng/author/muhd-shafiu-saleh/
    Gwamna Fintiri Ya Nada Sabbin Sarakuna 7 A Jihar Adamawa

MASU ALAKA

Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso
Manyan Labarai

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

June 24, 2026
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku
Manyan Labarai

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

June 24, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

June 24, 2026
Next Post
Hukunce-hukuncen Ganin Watan Ramadan

Hukunce-hukuncen Ganin Watan Ramadan

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.