ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Babbar Kasa Ita Ce Mai Jagorantar Sauran Kasashe Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Duniya

by CMG Hausa
3 years ago
Duniya

A baya-bayan nan ana ta samu karuwar rikici tsakanin bangarorin Isra’ila da Falasdinu, lamarin da ke haifar da asarar rayuka da jikkata da tsaiko ga harkokin ibada. Rikici tsakanin bangarorin biyu abu ne da yaki ci yaki cinyewa, wanda ke haifar da damuwa a yankin gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya.

A matsayinta na kasa mai burin ganin dunkulewar duniya cikin zaman lafiya da ci gaba, kasar Sin ta bakin firaministanta Qin Gang, ta ce za ta samar da yanayin da ya dace na ganin an samu sulhu tsakanin bangarorin biyu.

  • Kasar Sin Ta Soki Amurka Bisa Kakabawa Wasu Kamfanoninta Takunkumi Dangane Da Batun Maganin Fentanyl

Tabbas, lokaci ya yi da ya kamata a ce an samu mai shiga tsakani mai adalci, domin lalubo mafita da kawo karshen wannan daddaden rikici.

ADVERTISEMENT

Da yake tattaunwa jiya Litinin ta wayar tarho da takwarorinsa na Falasdinu Riad Maliki da na Isra’ila Eli Cohen, Qin Gang ya ce a shirye kasarsa take ta tallafawa tattaunawar wanzar da zaman lafiya tsakanin bangarorin tare da samar da damar cimma nasarar hakan.

Hakika burin Sin shi ne ganin an samar da zaman lafiya da hadin gwiwa da hakuri da girmama juna tsakanin kasa da kasa da al’ummunsu. Dole a samu bambance bambance tsakanin bangarori daban daban, amma kai zuciya nesa da hakuri da wadannan bambance-bambance, shi zai kai ga samun tabbatuwar zama lafiya a duniya da ma samun ci gaba.

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

Kasar Sin misali ce, domin ta kasance kasa mai kabilu da mabiya addinai daban-daban, amma abun ban sha’awa shi ne, yadda wadannan al’ummomi suka amince da yanayinsu kuma suke hakuri da juna, sannan suke morar zaman lafiya mai inganci.

Kasancewar na fito daga kasa mai mabanbantan kabilu da addinai, na kan yi matukar sha’awar yadda al’ummomin Sin ke zaune lafiya da juna ba tare da tsangwama ba. Don haka a ganina, babu kasar da ta fi dacewa wajen jagorantar sulhu tsakanin Falasdinu da Isra’ila, kamar kasar Sin.

Kamar yadda Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen dawo da dangantakar da ta yi tsami tsakanin Saudiyya da Iran, ina da yakinin za ta cimma nasara wajen shawo kan rikicin wadannan bangarori dake zaman makwabtan juna. Kuma a matsayin wadda ta tabbatar da zaman lafiya a cikin gida, na yi imanin idan har aka bata dama, Sin za ta iya gabatar da dabaru da matakai na shawo kan wannan rikici da yaki ci yaki cinyewa.

Lokaci ya yi da ya kamata sauran kasashen duniya su goyawa Sin baya kan wannan buri nata, a maimaikon bangaranci da rura wutar rikicin.

Matsayin babbar kasar da ta san ya kamata, shi ne jagorantar sauran kasashe wajen samar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa, kuma wannan, shi ne matsayin kasar Sin a duniya. (Faeza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara
Daga Birnin Sin

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
Daga Birnin Sin

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar APC Kan Kalubalantar Ingancin Zaben Abba Gida-gida

Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar APC Kan Kalubalantar Ingancin Zaben Abba Gida-gida

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.