A jiya Juma’a ne majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, wadda ita ce babbar majalisar dokokin kasar Sin, ta nuna rashin amincewa da kuma yin kakkausar suka ga yadda kasar Philippines ta bullo da abin da take kira dokar yankunan teku.
Kwamitin kula da harkokin waje na NPC ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, matakin wani yunkuri ne na kasar Philippines na aiwatar da hukuncin da aka yanke ba bisa doka ba a shekarar 2016 kan batun tekun kudancin kasar Sin, ta hanyar kafa dokokin cikin gida, kuma matakin ya keta ikon mulkin kan kasar Sin da hakkinta mai nasaba da teku a tekun kudancin kasar Sin.
- Yadda Donal Trump Ya Lashe Zaben Shugabancin Amurka
- Ofishin Jakadancin Faransa Da Hadin Gwiwar IITA Sun Horar Da Mata 500 Kasuwancin Noma
NPC ta bayyana cikin sanarwar cewa, kasar Sin tana da ikon mulkin kan kasa a tsibirin Nansha Qundao da ruwan da ke kusa da shi, da kuma tsibirin Zhongsha Qundao, ciki har da tsibirin Huangyan, da ruwan da ke makwabtaka da shi, kuma kasar Sin tana da ‘yancin kulwa da harkokin yankunan ruwa da abin ya shafa. Sin ta bukaci Philippines da ta gaggauta dakatar da ayyukanta masu sabawa doka, wadanda ke keta ikon mulkin kan kasar Sin da hakkinta masu nasaba da teku.
Hakazalika, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin a ranar Juma’a din ta fitar da wata sanarwa don nuna rashin amincewarta da dokar yankunan teku ta Philippines da kuma dokar layukan tekun tsibirai da ke karfafa ikirarinta game da harkokin teku a tekun kudancin kasar Sin. (Yahaya)