Za a kaddamar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin zafi, na daliban jami’o’i na duniya karo na 31, a ranar 28 ga watan Yulin nan a birnin Chengdu. Yayin wasannin motsa jikin na wannan karo, Nijeriya za ta tura ‘yan wasa 75, wadanda a yanzu haka ke kokarin kammala shiryawa.
Game da hakan, babbar sakatariyar kwamitin wasannin motsa jiki na daliban jami’o’in Nijeriya Chidiebere Ezeani ta bayyana cewa, ‘yan wasa da ita kan ta, suna da kyakkyawan fata game da wasannin motsa jikin na daliban jami’o’in da zai gudana a Chengdu, tana kuma da imanin cewa, birnin Chengdu zai gabatar da gasa mai ban mamaki ga duniya.
A cewar Ezeani, Nijeriya ta dade tana kokarin shiga wasannin motsa jiki na daliban jami’o’i, kuma ‘dan wasan kasar Clement Chukwu, ya ci nasarar lashe gudun mita 400 ajin maza a shekarar 1997, tare da kafa tarihin da har yau ba a karya shi ba.
Ezeani ta kuma jinjinawa ayyukan da kasar Sin ke gudanarwa yayin manyan gasannin motsa jiki na kasa da kasa, ta kuma yabi shirin gasar wasannin motsa jiki ta daliban jami’o’in Chengdu. Ta ce kwamitin shirya wasannin motsa jiki na daliban jami’o’in ya ba da goyon baya, da taimako ga tawagar Nijeriya, ba ma kawai ta samar da dandali da daliban jami’o’in Nijeriyar za su iya gwada kwarewarsu ba, har da ma samar da damammaki na cudanyar al’adun juna. (Safiyah Ma)