Bayan mako guda da ‘Yan Nijeriya suka kasance cikin duhu, Tashar samar da wutar lantarki ta kasa ta sake lalacewa.
An bayar da rahoton cewa wutar lantarki ta ragu daga megawatts 3,594.60 (MW) zuwa 42.7MW da misalin karfe 1 na daren ranar Talata.
- Na’urorin Tattara Wutar Lantarki Na TCN A Birnin Kebbi Sun Fashe
- Lantarki Ya Ɗauke A Faɗin Nijeriya, Yayin Da Tashar Samar Da Wuta Ta Ƙasa Ta Lalace
A cewar Guardian, tashar wutar lantarki ta Delta ce kawai ke aiki akan babbar tashar da 41.00MW a wuraren karfe 12 na rana yayin da Afam ke da 1.7MW.
Wannan na zuwa ne kwanaki biyar kacal bayan babbar tashar ta lalace sau biyu cikin sama da sa’o’i 12 da barin ‘yan Nijeriya daga cikin duhu.
Idan dai za a iya tunawa, an dawo da wutar lantarki a Nijeriya ‘yan sa’o’i bayan da aka daina jin duriyar wutar da aka yi a fadin kasar a ranar Alhamis din da ta gabata, sakamakon lalacewar na’urar samar da wutar lantarki ta kasa (TCN) daga Osogbo a jihar Osun.
Kwanaki kafin faruwar lamarin, Ministan wutar lantarki na Nijeriya, Adebayo Adelabu ya yi ikirarin cewa fashewar wani abu a Kainji/Jebba 330kV ne ya janyo lalacewar wutar lantarkin ta kasa da sanyin safiyar ranar Alhamis din da ta gabata.
Ministan ya bayyana hakan ne a cikin jerin sakonnin twitter da ya aike a dandalin X yayin da yake tabbatar da cewa dukkansu suna kan aiki don tabbatar da dawo da wutar lantarki cikin gaggawa.