• English
  • Business News
Tuesday, October 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Babu Dalilin Da Zai Sa ‘Yan Nijeriya Su Yi Talauci – Tinubu

byYusuf Shuaibu
2 months ago
inLabarai
0
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce ‘yan Nijeriya ba su da dalilin zama talakawa, yana mai jaddada kudirinsa na tabbatar da cewa ana bunkasa harkokin kasuwancin kanana da matsakaita a kasar nan.

Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin taron bunkasa harkokin kasuwanci kanana da matsakaita karo na 8 da ya gudana a Kalabar da ke Jihar Kuron Ribas a ranar Laraba.

  • Sin Ta Kara Yawan Tallafinta Ga Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinu
  • Ba Sulhu Ko Sassauci Ga Ƴan Bindiga A Zamfara – Gwamna Lawal Dare

Shugaban kasan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima, ya ce kasar na da dimbin albarkatun mutane da na ma’adanai wanda Allah ya albarkace ta da su.

Shugaban ya ce Kuros Ribas ta kasance a matsayin jihar da harkokin noma ke bunkasa wanda duk hatsi da aka suka yana tsirowa saboda kasar tana da taki.

Ya ce, “Gwamnatin tarayya tana shirin shuka itatuwan manja miliyan 100, fiye da kowanne jiha. Jihar Kuros Risan za ta fi amfana da wannan shirin,” in ji shi.

Labarai Masu Nasaba

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu

Tsaro: Gwamnan Kogi Ya Ayyana Yaƙi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Da ‘Yan Bindiga

Tinubu ya kara da cewa tun bayan karbar mulkinsa, gwamnatinsa ta bayar da fifiko wajen samun damar kudi kuma ta yi alkawarin tallafa wa harkokin kasuwanci da zai habbaka samar da ayyuka da samun kwarewa da kuma masana’antu.

Ya yaba wa gwamnatin Kuros Ribas kan kirkiro shirin tattaunawa da fasahar zamani a harkokin kasuwancin jihar, yana mai cewa wannan ya sa jihar ta yi fice a bangaren fasahar zamani.

“Fasahar zamani zai bai wa harkokin kassuwanci kanana da matsakaita samun damar intanet mai sauri da mai arha da kayayyakin aiki na zamani da samun hadin gwiwa don koyo da ingantawa, tare da tunawa cewa duniya ta kasance wani fage na bunkasa harkokin kasuwanci a zamanance.

“’Yan kasuwa da ke habaka kasuwancinsu a zamanance suna da wuri a Ikom da masu yin kayan daki a Kalabar da masu zanen kaya a Ogoja, Ugep, ko Odukpani.

“Wannan shi ne dalilin da ya sa tsare-tsaren gwamnatina na sabuwar fata ke nufin samar da yanayi mai kyau ga kanana da matsakaitan karkokin domin su samu damar habaka.

“Kudurinmu ba shi ne, ba kawai bayar da rance ko tallafi ba, gina wani tsarin da zai samar da ababen more rayuwa da kuma karfafa basirar ‘yan kasuwa,” in ji shi.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kuros Ribas, Bassey Otu ya bayyana taron harkokin kasuwanci kanana da matsakaita karo na 8 a matsayin matsayin wata manufa mai matukar muhimmanci a tsakanin jihar da gwamnatin tarayya.

Otu ya ce manufar ita ce inganta ruhin harkokin kasuwanci na ‘yan kasa da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.

Tags: Talauci
ShareTweetSendShare
Yusuf Shuaibu

Yusuf Shuaibu

Related

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu
Labarai

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu

4 hours ago
Tsaro: Gwamnan Kogi Ya Ayyana Yaƙi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Da ‘Yan Bindiga
Labarai

Tsaro: Gwamnan Kogi Ya Ayyana Yaƙi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Da ‘Yan Bindiga

6 hours ago
Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya
Labarai

Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya

7 hours ago
Next Post
Gasar Wasannin Mutum Mutumin Inji Ta Duniya Ta 2025 Na Gabatar Da Sabbin Fasahohin Zamani

Gasar Wasannin Mutum Mutumin Inji Ta Duniya Ta 2025 Na Gabatar Da Sabbin Fasahohin Zamani

LABARAI MASU NASABA

Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Na Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Korea Ta Arewa

Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Na Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Korea Ta Arewa

October 7, 2025
Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane

Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane

October 7, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu

October 7, 2025
Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

October 7, 2025
Tsaro: Gwamnan Kogi Ya Ayyana Yaƙi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Da ‘Yan Bindiga

Tsaro: Gwamnan Kogi Ya Ayyana Yaƙi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Da ‘Yan Bindiga

October 7, 2025
Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya

Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya

October 7, 2025
Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

October 7, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026

October 7, 2025
Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

October 6, 2025
Kada Ku Yi Sanadiyar Rugujewar Matatar Mai Ta Dangote – Shettima Ga PENGASSAN 

Kada Ku Yi Sanadiyar Rugujewar Matatar Mai Ta Dangote – Shettima Ga PENGASSAN 

October 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.