• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

“Babu Gaskiya A Takardar Da Ke Alaƙanta Gwamnatin Zamfara Da ’Yan Bindiga”

by Musa Muhammad
1 year ago
Zamfara

Wata tarkardar ƙage, wacce aka ce ta fito ne daga gidan gwamnatin jihar Zamfara da ke Gusau, mai ɗauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Abubakar Nakwada, ta yi iƙirarin cewa Gwamna Dauda Lawal ya bayar da umurnin a saki Naira Biliyan 1,378,000,000 ga wasu manyan shugabannin ’yan bindiga.

Haka zalika, takardar ta yi zargin cewa kafafen yaɗa labarai irin su Sahara Reporters, Jackson Ude, da sauran su sun amfana da waɗannan kuɗaɗe.

  • Sojoji Sun Sheƙe Ƴan Ta’adda Masu  Yawa A Kaduna Da Zamfara
  • Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Tallafawa Majinyata 1000 Da Abinci Da Kuɗi

To amma yana da muhimmanci a fahimci cewa, dukkan waɗanda aka yi wa ƙazafi a cikin wannan takardar sharri, su ne waɗanda suka ɗauki labaran fallasa alaƙanta Bello Turji da Alhaji Bello Mattawalle, Ministan Tsaro, da badaƙalar Alhaji Bashir Hadejia da aka kama da laifin ɗaukar nauyin ta’addanci da safarar makamai da zinare da dai sauransu.

Wannan ne ta sa Sakataren gwamnatin Jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Nakwada, yayin da yake mayar da martani kan wannan takarda, ya ce “Wannan takarda mara tushe ta alaƙanta gwamnatin Zamfara da kiran zaman lafiya da Bello Turji, wanda ya kasance sanannen shugaban ’yan bindiga ne ya yi.

Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta yi kakkausar suka, inda ta musanta yin sulhu da ‘yan ta’adda, kuma ta jaddada cewa takardar, wani yunƙuri ne da aka ƙirƙira da gangan da nufin gurgunta ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi na samar da tsaro.

LABARAI MASU NASABA

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

Don haka a fahimci wannan labarin da cewa ƘARYA ce, kuma yaudara ce.

Ita ma jam’iyyar AAC ta Omoyele Sowore, wanda kuma shi ne mawallafin jaridar Sahararepoters, wacce kuma tana cikin waɗanda aka ce sun amfana da waɗannan kuɗaɗe, ta fito fili ta yi tofin Allah-tsine da ganin wannan takarda, wacce ta ce ƙarya ce tsagwaronta.

Ɗan takarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar ta AAC, wanda ya ke kuma shi ne shugabanta, Omoyele Sowore ya ce, “Ya wajaba a gare mu mu nusar da jama’a irin sabon salon farfagandar da Bola Tinubu ya fito da ita na zubar da mutuncin mani da mutunci, ni da SaharaReporters.

“Wata takardar cikin gida, wacce aka alaƙanta da Sakataren gwamnatin jihar Zamfara, tana nan tana yawo a tsakanin jama’a, aka ce wai an ware wasu maƙudan kuɗaɗe don a raba wa ‘yan ta’adda da wasu kafafen watsa labarai.

Sowore ya ce, wannan ƙarya ce, bai san da wani abu mai kama da haka ba.

Shi ma, ɗaya daga cikin waɗanda aka ambaci sunayen su a waccan ƙagaggar takarda, Jacson Ude, a shafin sa na tweeter (X), ya yi watsi da wannan batu, inda ya ɗora laifin kan tsohon Kwamishinan yaɗa labarai na gwamnatin Bello Matawalle.

Jackson Ude ya yi zargin cewa Tsohon Kwamishinan yaɗa labaran, ya kasance ya ɓoye kansa a wani wuri, inda ba abin da ya ke yi sai ƙage-ƙagen ƙarairayi kan duk waɗanda suka ya ƙi gwammatin Matawalle.

Don haka ya ce, wannan takarda sam ba ta da tushe balle makama, ƙarya ce tsagwaronta.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati
Labarai

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba
Labarai

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta
Manyan Labarai

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Next Post
Kungiyar Miyatti Allah Ta Haramta Kiwon Dare A Jihar Kwara

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.