Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa, ya ce “ya fi ‘yan Nijeriya shan wahalar tsadar rayuwa”.
Ɗangote ya tabbatar wa da ‘yan ƙasa cewa, wasu ne suka ɗauki nauyin yaɗa labarin domin ɓata masa suna a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke cikin halin ‘ƙaƙa-ia-ƙayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su.
- Zanga-zangar Minna: Shugaba Tinubu Ya Ba Da Umarnin A Sassauta Farashin Kayan Abinci – Idris
- Me Ya Sa Babur Da Kasar Sin Ta Samar Yake Samun Karbuwa
Sanarwar ta nemi ‘yan Nijeriya da su yi watsi da labarin, inda ya yi addu’ar fatan kawo ƙarshen matsalar da ake ciki a Nijeriya.
“Duk abin da ya shafi ‘yan Nijeriya ya shafe mu”, in ji Sanarwar.
“Mu ma muna sayen muhimman kayan abinci a kasuwa kamar yadda kowa ke saye don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen ciyar da al’umma,” in ji Ɗangote.
Shugaban kamfanin ya yi mamakin yadda ake neman haddasa saɓani tsakanin Kamfanonin Ɗangote da ɓangaren gwamnatin tarayya, inda ya ce, shi ɗan kasuwa ne, ba ɗan siyasa ba, don haka babu inda ya yi maganar ƙalubalantar Gwamnatin tarayya.
“Kamfanin mu ya kasance mai bin dokokin ƙasa a kodayaushe, tare da neman sauƙi ga al’umma da fatan alheri.”
Saboda haka, sanarwar ta nemi ‘yan Nijeriya su guji ɗaudar saƙon da yake ba daga kamfani kai tsaye ba, tare da daina yaɗa raɗe-raɗi da jita-jita.