• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Babu Kasar Da Za Ta Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tabbatuwar Tsaro Ba

by CMG Hausa
2 years ago
Tsaro

An fara gudanar da taron dandalin tsaro da zaman lafiya na Sin da Afrika karo na 3, daga jiya Litinin zuwa ranar Asabar, a wani yunkuri na tabbatar da tsaro da kaucewa babakeren manyan kasashen yamma.

Har kullum Sin ta kasance mai taka rawar gani game da abubuwan da suka shafi ci gaban Afrika; ciki har da tsaro, bisa girmama muradu da ’yancin kasashen Afrika kana ba tare da gindaya wasu sharudda na siyasa ba. Kasashen Afrika sun riga sun san yadda kasashen yamma suke fakewa da tallafin tsaro wajen tsoma baki cikin harkokinsu na gida kuma ba tare da tabuka abun kirki ba, sai ma yi musu zagon kasa da ta’azzara yanayin da suke ciki maimakon samar da zaman lafiya.

  • Bai Dace A Kalubanci Dokar Tsaron HK Ba

Kasar Sin ta yi kuma an gani sabanin wadancan kasashe. Wato ta dauki matakan tabbatar da tsaro bisa kalubalen da ta fuskanta, kuma za ta iya bugin kirji ta ce lallai kwalliya ta biya kudin sabulu, inda ta shafe shekaru da dama ba tare da fuskantar harin ta’addanci ko wasu munana laifukan tsaro ba, shin kasashen yamma za su iya alfahari kamar Sin?

Matsalolin tsaro da kasashen Afrika suke fuskanta da suka hada da na ta’addanci da kabilanci da na ’yan aware, sun yi kama da irin wanda Sin ta taba fuskanta, kuma zuwa yanzu, matsalolin sun zama tarihi a kasar.Bisa wadannan dalilai nake ganin, babu wadda ta fi dacewa ta koyar da dabarun tabbatar da tsaro kamar kasar Sin, la’akari da dimbin kamaceceniyar dake akwai tsakaninta da kasashen Afrika. Na ziyarci bangarori da dama na kasar Sin, kuma na ganewa idona dimbin ci gaban da kasar ta samu, wanda ba ya rasa nasaba da tabbatuwar tsaro da zaman jituwa tsakanin kabilu daban-daban na kasar. Don haka, babu wani dalili da zai hana kasashen Afrika tabbatar da tsaro muddun suka yi watsi da yaudarar kasashen yamma tare da dauka da aiwatar da darasin da Sin za ta samar, lamarin da kuma zai kai su ga samun ci gaban da suke muradi. (Faeza Mustapha)

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025
Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa
Daga Birnin Sin

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

October 24, 2025
Next Post
Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Gabon

Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Gabon

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

October 25, 2025
Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025
Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa

October 25, 2025
Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi

October 25, 2025
Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.