Tsohon gwamnan Jihar Ribad, Nyesom Wike, ya ce babu wata matsala idan Majalisar Dokokin Jihar Ribad ta tsige Gwamna Siminalayi Fubara.
A wata hira da ya yi da manema labarai ranar Laraba a Abuja, Wike ya ce majalisar na da hurumin tsige gwamnan, domin ya aikata laifuka da suka dace a tsige shi, ciki har da rashin biyan albashin ‘yan majalisar na tsawon watanni.
- Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [5]
- Yadda Sinawa Ke Tabbatar Da Hakkinsu Na Demokuradiyya A Tafarkin Manyan Tarukan NPC Da CPPCC
“In dai mutum ya aikata abin da ya saɓa wa doka, kuma majalisa ta ga ya dace a tsige shi, to babu laifi a hakan. Kundin tsarin mulki ya tanadi hakan,” in ji shi.
Wike, wanda a yanzu shi ne Ministan Abuja, ya musanta ra’ayin da ke cewa tsige Fubara zai haddasa rikici a jihar.
“Mutane na cewa idan an tsige shi, za a samu hargitsi da rashin zaman lafiya. Wannan shirme ne. Babu abin da zai faru,” in ji shi.
Gwamna Fubara da Wike sun samu saɓani tun bayan hawa mulki, lamarin da ya haddasa rikici a siyasar Jihar Ribas, wacce ke da arziƙin man fetur.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp