Gwamnatin Jihar Kaduna ta musanta bayanan da ke cewa an yi sulhu tsakanin al’ummar Hausawa da Fulani da kuma Koro a karamar hukumar Kagarko sanadiyyar rashin jituwa da ke tsakanin su.
Gwamnatin ta bayyana haka ne cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Litinin, wadda ta samu sa hannun Muhammad Lawal Shehu, mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanata Uba Sani.
Sanarwar ta ce tana jan hankalin al’umma daga wasu rahotannin da babu gaskiya a cikin su, wadanda ke bayyana cewa ministar mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta yi wani zaman shiga tsakani da manyan kabilun, a wani yunkuri na kawo karshen rikicin da aka kwashe shekara 20 ana fama da shi a yankin.
Sai dai sanarwar ta bayyana cewa “Kagarko na daga cikin kananan hukumomi mafiya kwanciyar zaman lafiya da lumana a jihar, kuma an kwashe shekaru ba tare da wani rahoton na rikici a karamar hukumar ba.”
Sanarwar ta ce wasu tsirarun mutane ne suka tunkari ministar da batun, kawai domin cimma wasu muradunsu.