Karamin ministan tsaro, Hon. Bello Mohammed Matawalle, ya shelanta cewa gabaki daya babu sauran burbushin tsagerun Lakurawa a yankin Arewa Maso Yamma a halin yanzu.
Da yake ganawa da manema labarai a Gusau a ranar Lahadi, tsohon gwamnan Jihar Zamfara ya ce, dakarun sojoji sun hallaka gungun ‘yan ta’addan, sannan sun kuma tarwatsa sansanoninsu da kwato bindigogi da alburusai daga hannunsu.
- Yadda Turmutsutsin Rabon Kayan Abinci Ya Dagula Karsashin Kirsimeti
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Dama Tare Da Tarwatsa Sansanoninsu A Katsina
Ya kuma ce wadannan ‘yan ta’addan ba ma ‘yan Nijeriya ba ne, sun fito ne kawai daga Burkina Faso da Mali domin su janyo tashin tashina a Nijeriya.
“Mun gama da su a yankin Arewa maso yamma. Duk wanda ke magana kan tsagerun Lakurawa yana yi ne kawai domin ya bata kima da mutuncin gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro,” ministan ya shaida.
Ya ci gaba da cewa, mutane kawai sun dukufa wajen yayada labarai na kanzon kurege domin sanya razana da firgici a zukatan al’umma, sai ya kalubalanci ‘yan jarida musamman ‘yan Soshal Midiya da su daina amincewa da irin wadannan ikirarin ba tare da tantance bayanan ba.
“A kullum sojoji na kashe ‘yan fashin daji da ‘yan bindiga dadi. Amma ba za ka ga masu s’ocial media’ na yayata hakan ba.
“Muna sane mazauna kauyuka na bai wa ‘yan jarida bayanai marasa tushe kan ayyukan masu garkuwa da mutane ake a jihar nan domin nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
“Amma ba za mu mika wuya ga barazanarsu ba. Gwamnatin Tinubu a shirye take ta kawo karshen dukkanin ‘yan fashin daji a Arewa maso yammacin kasar nan a karshen 2025.
“Kare rayuka da dukiyar al’umma shi ne muhimmin abu da gwamnatin tarayya ta sanya a gaba, kuma za mu kara sanya azama kan wannan manufar,” ya shaida.
Ministan ya nemi ‘yan Nijeriya da su yi fatali da labarai karya da makiyan zaman lafiya da ci gaban kasar nan ke yadawa.