Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya sake nanata cewa sabbin masarautu hudu da gwamnatinsa ta kirkiro suna nan daram.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin bikin ranar ma’aikata da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.
- An Kwaso Daukacin Daliban Nijeriya Da Suka Makale A Khartoum – Kungiyar Dalibai
- Gwamnatin Edo Za Ta Kashe Naira Biliyan 6 Wajen Gyaran Makarantun Sakandare A Jihar
Kalaman nasa na zuwa ne kwanaki kadan bayan da jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana a wani faifan bidiyo cewa gwamnatin Abba Yusuf mai jiran gado za ta sake duba salon mulkin masarautun Kano.
Sai dai Gwamna Ganduje wanda ya raba masarautun Kano gida biyar sannan ya tsige Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na wancan lokacin ya bayyana cewa sabbin masarautun guda hudu alama ce ta hadin kai, ci gaba da jin dadin al’umma.
Ya kara da cewa an kirkiro masarautun ne domin karrama al’ummar yankunan da kuma dawo da martabar masarautun gargajiya.
“Duk wanda ya ziyarci hedikwatar wadannan sabbin masarautun zai yarda cewa mun kawo ci gaba a wadannan wuraren. Mun kirkire su ne domin karrama mutanen wadannan yankuna,” in ji Ganduje.
Ya kuma tabbatar wa da al’ummar Kano cewa masarautu na dindindin ne kuma sun zo su zauna, ya kuma kara da cewa duk wanda ya yi yunkurin rusa su Allah ba zai kawo shi Jihar Kano ba.
“Ko ba ma gwamnati muna addu’a kuma za mu ci gaba da addu’ar Allah ya kare wadannan masarautun daga dukkan sharri. Na gode muku duka,” in ji shi.
Samar da sabbin masarautun dai ya kasance batun cece-kuce a Kano tun daga 2020, inda wasu ke goyon bayan matakin yayin da wasu ke adawa da shi.