Gwamnatin tarayya ta gargadi duk masu shirin kawo tarnaki ga tsarin mika mulki da shugaban kasa mai ci Muhammadu Buhari zai yi ga zababben shugaban kasa, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.
Sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha shi ya yi wannan gargadin a ranar Talata a Abuja, yayin da yake bayani kan ayyukan kwamitin mika mulki na shugaban kasa, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa tsarin mika mulki ya kankama, kuma a ranar 29 ga watan Mayu za a mika mulki ga sabon shugaban kasar cikin lumana.
Ya kuma bayyana cewa bayan ayyana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa, kwamitin mika mulki ta bukace shi da ya zabo wakilansa ga majalisar kamar yadda dokar zartarwa ta tanada.
Don haka, Mustapha ya ce zababben shugaban kasa ya zabi Atiku Bagudu, Gwamnan Jihar Kebbi da kuma Cif Olawale Edun wadanda tun daga lokacin suka shiga aikin gadan-gadan.
Ya kuma bayyana cewa a yanzu haka zababben shugaban kasa ya tare a gidan tsaro, sannan kuma an tura jami’an tsaro na ma’aikatar harkokin wajen kasa da na ‘yan sandan Nijeriya zuwa ga zababben shugaban kasa da mataimakinsa.
Da yake magana kan barazanar da wasu ke yi na cewa mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu ba za ta tabbata ba, ya ce an samar da dukkan matakan tsaro domin dakile duk masu shirin tayar da fitina, yana mai cewa duk wanda bai gamsu da yadda zaben ya gudana ba, ya kamata su fitar da korafe-korafensu ta hanyar kotu.
Ya ce: “Tsarin mika mulki yana kan gaba kuma da yardar Allah za a mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu, lamari ne da ya shafi tsarin mulki, kuma duk wasu kararraki ko an warware ko kuma ba a warware su ba, ba za su hana mika mulki a hukumance ba.
“Shugaba Buhari ba zai kara ko kwana guda ba bayan ranar 29 ga watan Mayu, zai mika wa duk wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana a matsayin zababben shugaban kasa. Kotu za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na yin hukunci na wadannan shari’o’in ko da bayan rantsar da sabon shugaban kasa. Ba wannan ne karon farko da muke gudanar da zabe ba, wannan ba shi ne karon farko da mutane ke karbar mukamai da kararraki ba.
“Batutuwan da ke gaban sauraran kararrakin zabe za su ci gaba da tafiya ba tare da wata matsala ba har sai an yanke hukuncin karshe a kotun koli, kuma bangarorin da abin ya shafa za su gamsu da hukunci a kowane mataki na kararrakin.
“Muna yin komai don ganin cewa tsarin mika mulki bai darkushe ba. Gwamnatin tarayya ta yi wani bayani kan hakan. Jami’an tsaro da wani bangare na masu leken asiri na kwamitin mika mulki na shugaban kasa za su yi duk abin da zai tabbatar da cewa babu abin da ya faru da zai kawo cikas ga tsarin mika mulki cikin lumana,” in ji sakataren gwamnatin tarayya.