Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya tabbatar da cewa Laftanar Ahmad Yerima, jami’in sojan ruwa da ya yi musayar kalamai da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ba zai fuskanci wani matakin ladabtarwa ba.
Matawalle ya bayar da wannan tabbacin ne a wata hira da ya yi da DCL Hausa bayan jita-jitar da jama’a ke yi game da cewa, akwai yiwuwar Yerima ya fuskanci kwamitin ladabtarwa bayan wani bidiyo na rikicinsa da Wike ya yadu a shafukan sada zumunta.
- Zaɓen 2027: Jam’iyyar ADC ta Ƙaddamar Da Kwamitin Sake Fasalinta A Kaduna
- Lambar Yabo Da LEADERSHIP Ta Ba Mu, Ta Ƙara Zaburar Da Mu – Gwamna Sule
A cikin bidiyon, wanda aka dauka a lokacin ziyarar Wike zuwa wani fili da ake takaddama a kansa a gundumar Gaduwa, Abuja, an ga ministan FCT yana musayar kalamai masu zafi da matashin jami’in sojin ruwa, wanda ya tsaya tsayin daka akan aikinsa.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, ministan FCT ya je filin mai lamba 1946 a ranar Litinin inda ya zargi sojoji da hana jami’ai daga Ma’aikatar Kula da Ci Gaban FCT aiwatar da umarnin dakatar da aiki a filin.
Ana zargin cewa, filin yana da alaka da tsohon Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo (mai ritaya). Don haka, sojojin da ke wurin suka hana ministan shiga wurin, wanda hakan ne ya haifar da saɓanin. Daga baya, Wike ya yi ikirarin cewa, masu ginin ba su da takardu masu inganci ko izinin doka don gina wurin.
Da yake mayar da martani ga lamarin, Matawalle ya ce, ya kamata a magance lamarin ta hanyoyin da suka dace maimakon ta hanyar rikici a bainar jama’a.
Ya yaba wa Yerima da ya kwantar da hankalinsa a lokacin rikicin, yana mai bayyana halayensa a matsayin mai ladabi kuma ƙwararre.













