Rundunar ‘yansandan Jihar Filato, ta musanta fashewar bam a kasuwar Terminus da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a babban birnin jihar.
Wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Alfred Alabo, ya fitar, ta ce bayan samun rahoton wani rami mai zurfi da ake zargin an dasa abu mai fashewa a jikin katangar tsohon JUTH da ke kan titin Murtala Muhammad, wanda ya haifar da firgici tsakanin al’umma.
- Mutane 6 Sun Rasu Sakamakon Ruftawar Ramin Haƙar Ma’adinai A Filato
- ‘Yan Bindiga 3 Da Mai Yin Safarar Makamai Sun Shiga Hannu A Taraba
Da samun rahoton, ya ce, nan take Kwamishinan ‘yansandan, ya umarci jami’in da ke kula da sashen hada bama-bamai na tawagar ƙwararru zuwa wajen don tantance halin da ake ciki tare da daukar matakan da suka dace wanda aka gano ramin ba ya ɗauke da wani abun fashewa.
A halin da ake ciki, Kwamishinan ‘yansandan, Olugbemiga Adesin, ya ziyarci wajen don gane wa idonsa abin da ya faru.
Ya yaba wa al’ummar bisa haɗin kai da suka bayar ga jami’an tsaro tare da kira gare su, su ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu na yau da kullum ba tare da fargaba ba ko barazana ga rayuka da dukiyoyi ba.