Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa babu wani dan arewa mai hankali da yi wa APC yakin neman zabe a 2027, saboda ‘yan Nijeriya sun gaji da salon mulkin APC.
Babbar jam’iyyar adawar dai na mayar da martani ne kan zargin rashin yin aiki da Sanatan Kaduna ta tsakiya, Lawal Adamu, da kuma zargin dakatar da rabon kayayyakin koyo da koyarwa na miliyoyin naira da dan majalisar ya sayo, wanda aka ce gwamnatin jihar ta dakatar da shi.
- CMG Ya Kaddamar Da Gasar Basirar Mutum-mutumin Inji Ta Duniya
- Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Janye Bincike Kan Shigo Da Jan Karfe
Babban mataimaki na musamman ga shugaban jam’iyyar PDP na kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa, Yusuf Dingyadi shi ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai, cewa ya kamata gwamnan jihar ya hada kai da sauran wakilan jama’a domin amfanin jihar.
“Ana sa ran gwamnatin jihar ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasa ba, za ta hada kai da sauran zababbun wakilan jama’a domin inganta rayuwar al’ummar Kaduna.
“Suna daukar hayar masu yada farfagandar siyasa, ta hanyar amfani da kafafen yada labarai na rediyo da na sada zumunta, suna zargin Sanata Lawal Adamu da rashin aikin yi.
“PDP jam’iyyar siyasa ce, kuma muddin kuka ci gaba da kai mata hari, ba za ku samu ci gaba ba. Ba za ku iya daukar nauyin ‘yan baranda na siyasa da farfaganda don lalata mana kima ba don kawai burge Shugaba Bola Tinubu saboda ajandar ku ta 2027.
“Ba wani dan Arewa mai hakali da zai yi wa APC yakin neman zabe a Arewa. Kasancewar wasu ’yan siyasa suna yi wa jam’iyyar shigo ba zurfi ne domin su sami abun sawa a bakin salati ne kadai amma ba wai za su zabe ta a 2027 bane.
“Bai kamata Uba Sani ya bar wasu ‘yan siyasa suna yaudararsa, wadanda ba za su iya amfanar da siyarsa da komai ba.
“Saboda haka, ‘ya’yan jam’iyyarmu da aka zaba a PDP ba su kwanta barci ba. Suna aiki tukuru a mazabarsu fiye da na APC.
“Ba za ku iya yin amfani da nasararmu ta siyasa ta hanyar tallafa wa masu yada farfaganda don bata zababbun ‘yan majalisarmu ko ta hanyar sauya sheka a zai yi tasiri ba,” in ji Dingyadi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp