Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce babu wani gungun mutane da suke juya Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta bayan fage, abin da a turance ake ce wa “cabal”.
A cewar sa, wannan Shugaban Ƙasar mai ‘yancin kan sa ne, wanda ke sauraron ra’ayoyi da dama amma a ƙarshe yana yanke shawara bisa abin da ya fi amfanar da ƙasar nan.
- Mummunan Hatsarin Mota Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 19 A Kogi
- Amarya Ta Kashe Uwargida Bayan Ta Daɓa Mata Wuƙa A Katsina
Idris ya faɗi hakan ne a ranar Alhamis a Abuja yayin da yake jawabi a Taron Ƙasa na Jam’iyyar APC da aka gudanar ƙarƙashin taken “Shirin Sabunta Fata: Tafiyar Da Aka Yi Zuwa Yanzu.”
Ya ce: “Ya kamata ku nazarci Shugaban Ƙasa sosai. Za ku iya faɗin ra’ayoyin ku; zai saurare ku, amma a ƙarshe shawarar da zai yanke tasa ce. Ina ganin ya dace mu gane hakan.”
Yayin da yake bayani kan taken taron, ministan ya ce Shugaba Tinubu na da cikakkiyar niyya wajen aiwatar da Shirin Sabunta Fata — wanda tsari ne da ya mayar da hankali kan jin daɗin talaka da fitar da cikakken ƙarfin Nijeriya.
“Shirin Sabunta Fata na da nufin kawo sauyi mai ma’ana ga rayuwar al’ummar Nijeriya ta hanyar muhimman matakai da za su fitar da cikakken ƙarfin Nijeriya, ta hanyar da ba a taɓa gani ba,” inji ministan.
Idris ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya karɓi mulki ne a lokacin da Nijeriya take cikin mawuyacin hali, amma ya ɗauki matakai da gaggawa tun daga farko.
Ya ce: “Daga cikin abubuwan farko da Shugaban Ƙasa ya aikata su ne aiwatar da cire tallafin mai da cire tallafin musayar kuɗi, waɗanda suka daɗe suna hana cigaban Nijeriya, suna haifar da asarar biliyoyin daloli a duk shekara.”
Ya ƙara da cewa sakamakon waɗannan sauye-sauyen yanzu ya fara bayyana a fannoni da dama kamar ababen more rayuwa, harkar ma’adinai da ta man fetur.
“A matakin tarayya, ƙarin kuɗaɗen shiga sun buɗe ƙofofi ga manyan ayyukan ababen more rayuwa,” inji shi.
Ya lissafa wasu manyan hanyoyi guda huɗu — hanyar Legas zuwa Kalaba, da hanyar Sakkwato zuwa Badagiri, da hanyar Kalaba zuwa Abuja da hanyar Akwanga-Jos-Bauchi-Gombe — waɗanda suka haura kilomita 2,600.
Ya kuma ambaci aikin layin dogo na Kano zuwa Kaduna a matsayin muhimmin tsari a ƙarƙashin Shirin Sabunta Fata da kuma sashe mai muhimmanci na shirin layin dogo daga Legas zuwa Kano.
A ɓangaren gidaje, ya ce an ƙaddamar da ayyukan Birane da Gidajen Shirin Sabunta Fata domin rage giɓin gidaje a ƙasa, da ƙirƙirar ayyukan yi da farfaɗo da birane.
Don tallafa wa bunƙasar tattalin arziki na zamani, Idris ya ce Gwamnatin Tarayya na shimfiɗa wayoyin intanet har kilomita 90,000 a faɗin ƙasar nan.
Ya bayyana wannan yunƙuri da cewa, “matakin shimfiɗar ‘broadband’ da ba a taɓa yi ba zai rufe giɓin intanet a ƙasa, ya tallafa wa mulkin zamani, ya jawo jari na fasaha, da kuma bai wa sassa kamar ilimi, lafiya da kasuwanci damar amfani da sana’o’in intanet.”
Ya bayyana cewa sama da ɗalibai 300,000 ke amfana da Asusun Rancen Ilimi na Ƙasa (NELFUND), sannan ma’aikata na amfani da sabon Tsarin Lamunin Kayayyaki domin sayen muhimman abubuwan buƙata.
A fannin tsaro, Ministan ya ce: “Sojojin mu sun kashe dubban ‘yan ta’adda tare da ceto kusan mutane 10,000. An samu sababbin jiragen sama fiye da 25, yayin da Rundunar Sojan Ruwa ta karɓi sababbin jiragen ruwa guda huɗu.”
Ya yaba wa Shugaban Ƙasa bisa kafa Ma’aikatar Raya Kiwo da kuma kafa Hukumomin Raya Yankuna a kowane yanki shida na ƙasar, domin farfaɗo da noma da tabbatar da cigaban da ya shafi kowane yanki.
Ministan ya jaddada cewa Shirin Sabunta Fata tsari ne mai cike da kulawa ga rayuwar al’umma.
Ya ce: “A ƙarshen kowane shiri da manufofin gwamnatin Tinubu akwai ɗan Nijeriya talaka wanda rayuwar sa ke samun sauyi mai kyau. Ɗan Nijeriya da ke samun damar samun kuɗi don kan sa ko kasuwanci; ɗan Nijeriya da ke ganin farashin abinci yana sauka; ɗan Nijeriya da ke amfani da hanyoyin sufuri masu arha ta hanyar iskar gas ta CNG; ɗan Nijeriya da ke samun wutar lantarki ta hanyar ɗaya daga cikin shirye-shiryen wutar lantarki na gwamnati; ɗan Nijeriya da ɗan sa ko ‘yar sa ke samun damar zuwa jami’a ta hanyar NELFUND.”
Idris ya kuma ambaci manufar ‘Renewed Hope Nigeria First’ da aka zartar kwanan nan wadda ke wajabta wa dukkan ma’aikatun gwamnati su fifita amfani da kayan Nijeriya da ayyuka da ƙwarewar ‘yan ƙasa wajen kashe kuɗin gwamnati.
Ya ce: “Wannan abin tarihi ne da ba a taɓa samun irin sa ba, da burin ƙarfafa masana’antu ta hanyar samar da kaya a gida da kuma kare tattalin arzikin Nijeriya daga girgizar da ke faruwa a duniya.
“Shugaban mu, muna maka godiya da samun wannan tsari na kishin ƙasa, da kuma ginin tubalin farfaɗo da tattalin arzikin Nijeriya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp