Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya bayyana cewar, shi kam, babu wata baraka a tsakaninsa da magabacinsa da ya amshi mulki a hannunsa, Sanata Henry Seriake Dickson sabanin yadda wasu jama’a ke ta yadawa.
Diri, wadda ke maida martani kan jita-jitan ya yi bayanin cewa yana matunta wadanda suka gabaceshi musamman ma Dickson wanda ya mika masa mulki.
- Amurka Ce Ke Yi Wa Zaman Lafiya A Zirin Taiwan Barazana
- Wang Yi Ya Yi Cikakken Bayani Kan Matsayar Sin Game Da Yankin Taiwan
Gwamnan ta bakin kakakinsa Mista Daniel Alabrah, a wata sanarwar da ya fitar a ranar Asabar, ya kara da cewa, alakarsa da magabacinsa a dinke take na ta barke ba.
Ya ce, “A ‘yan kwanakin nan sakamakon karatowar lokacin zabe, wasu mutane da wasu kungiyoyi sun dukufa yayata abubuwan da suke tunani a cikin ransu.
“Damuwarsu dai sai sun haifar da rashin fahimta a tsakanina da wanda na gaji mulki a hannunsa, Senator Seriake Dickson da kuma cikin jam’iyyar mu ta PDP.
“Da gangan na zabi yin shiru na yi kunnen uwar shegu da irin wannan labaran soki-burutsun da ake yadawa a kafafen sadarwa zamani da wasu kafefen yanar gizo.”
“Lura da dabi’una da manufofin Gwamnatina, na tsawatar wa hadimaina a fannin yada labarai da kada su shiga amsa irin wannan labaran da ake yi don cimma wata manufa.
“Daya daga cikin nauyin da ke kaina shine na yi kokarin bunkasa hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar Bayelsa da kyautata shugabanci gami da kawo ayyukan inganta jiharmu.”
Diri ya kara da cewa masu yayata jita-jitan suna da manufar kawu rabuwar kawuka ne, “Domin ma kauce wa kowace irin kokonto ni kam babu wata baraka a tsakanina da wanda na gaji mulki a hannunsa kuma akwai mutunta juna a tsakaninmu.”
Daga bisani gwamnan ya roki jama’a da su yi watsi da masu yada hakan tare da kira ga jama’an jihar da su kara Bada hadin kai domin tabbatar da cigaban jihar a kowani lokaci.